"Dole a Cika Su"; Iran Ta Gindaya Sharudda 2 Kafin Fara Tattaunawa da Amurka

"Dole a Cika Su"; Iran Ta Gindaya Sharudda 2 Kafin Fara Tattaunawa da Amurka

  • Kasashen Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shirin fara tattaunawa bayan cimma yarjejeniyar tsagaita a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa dole ne san cika wasu sharudda biyu kafin a fara tattaunawar
  • Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa daya daga cikin sharuddan shi ne dole a tsagaita wuta kan hare-haren da ake kai wa a Lebanon

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohmmad Bagher Ghalibaf, ya yi magana kan tattaunawa da Amurka don zaman lafiya.

Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa ba za a fara tattaunawa ba har sai an tsagaita wuta a Lebanon.

Iran ta kafa sharudda kan tattaunawa da Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B
Source: Getty Images

Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Awanni kafin shiga zauren tattaunawa, JD Vance ya fallasa shirin da Amurka ta yi wa Iran

Wadanne sharudda Iran ta gindaya?

Shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa ba za a iya fara tattaunawa da Amurka ba har sai an cika wasu sharuɗɗa guda biyu.

Ya bayyana cewa dole ne a tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon da kuma sakin kuɗaɗen Iran da aka rike.

“Matakai biyu da ɓangarorin biyu suka amince da su har yanzu ba a aiwatar da su ba: tsagaita wuta a Lebanon da kuma sakin kadarorin Iran da aka rike kafin a fara tattaunawa."

"Dole ne a cika waɗannan abubuwa biyu kafin tattaunawa ta kankama.”

- Mohammad Bagher Ghalibaf

Iran na son a tsagaita wuta a Lebanon

Hakazalika, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce dole ne Amurka ta cika alƙawarin tsagaita wuta a Lebanon.

Abbas Araghchi, ya ce dole ne Amurka ta cika alƙawuran da ta ɗauka na tsagaita wuta, waɗanda ya ce sun haɗa da tabbatar da cewa yarjejeniyar ta shafi ƙasar Lebanon.

Iran na son a tsagaita wuta a Lebanon
Ministan harkokin wajen Iran, Seyed Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta ce Araghchi ya yi waɗannan kalamai ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da zaɓaɓɓen jakadan Iran a Lebanon, Mohammad Reza Shibani.

Kara karanta wannan

Ministan Pakistan ya yi kaca kaca da Isra'ila kan zubar da jini a duniya

Ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Lebanon, waɗanda ya jaddada cewa ya kamata a ce sun tsaya bisa ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

Karanta wasu labarin kan Amurka, Iran

Fatan Amurka kan tattaunawa da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya yi magana kan shirin tattaunawar kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

JD Vance, ya bayyana cewa yana sa ran tattaunawar zaman lafiya da Iran za ta kasance mai kyau kuma ta haifar da 'da mai ido.

Vance ya kara da cewa Amurka a shirye take ta yi tattaunawa cikin gaskiya idan Iran ma ta nuna irin wannan niyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng