'Za Mu Ci gaba da Kai Hari,' Isra'ila Ta Sake Tsokano Iran da Ta Kashe Mutane a Lebanon

'Za Mu Ci gaba da Kai Hari,' Isra'ila Ta Sake Tsokano Iran da Ta Kashe Mutane a Lebanon

  • Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila za ta ci gaba da kai wa Hezbollah hari har sai 'yan Arewacin ƙasar sun samu tsaro
  • Akalla mutum 203 ne aka kashe a Lebanon sakamakon harin Isra'ila, wanda ya zama rana mafi muni tun bayan ɓallewar yaƙi a Fabrairu
  • Iran ta yi barazanar mayar da martani mai tsanani ga Isra'ila, lamarin da ake ganin zai iya rushe yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Amurka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila – Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin cewa ƙasarsa za ta ci gaba da kai hare hare kan Hezbollah "a duk lokaci da wurin da ya dace."

Wannan barazana ta Netanyahu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da Iran, duk da da Iran din ta ce akwai yarjejeniyar daina kai hari Lebanon.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Firaministan Isra'ila ya sake dauko rigima bayan dakatar da yakin Iran

Iran ta yi barazanar daukar fansa idan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Lebanon.
Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila (hagu), da birnin Beruit, Lebanon bayan harin IDF (tsakiya) da Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei (dama). Hoto: @MKhamenei_ir, @netanyahu/X, Getty Images
Source: UGC

Iran za ta ci gaba da kai hari Lebanon

Netanyahu ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X, inda ya jaddada cewa za su yi amfani da ƙarfin soja wajen murkushe duk wanda ke barazana ga fararen hular Isra'ila.

Wannan furuci na zuwa ne bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da munanan hare-hare a tsakiyar birnin Beirut na ƙasar Lebanon a ranar Laraba, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 203 tare da raunata wasu kusan 1,000.

A cikin sanarwar da ya fitar, Firaministan Isra'ila ya ce:

"A Beirut, mun kashe Ali Youssef Kharshi, sakatare kuma na hannun daman Naim Qassem, shugaban kungiyar ta'addanci ta Hezbollah.
"A lokaci guda kuma, da tsakiyar dare, IDF ta farmaki manyan kadarorin 'yan ta'addan a Kudancin Lebanon, gadojin da ake safarar dubunnan makamai, rokoki da kayan yaki zuwa hedikwatar Hezbollah.
"Sakonmu a bayyane yake: Duk wanda ya taba fararen hular Isra'ila, za mu farmake shi. Za mu ci gaa da kai hari kan Hezbollah a duk lokacin da bukatar hakan ta taro, har sai an samar da cikakken tsaro ga al'ummarmu da ke Arewa."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Iran ya fadi abin da ba za su taba kyalewa ba

Iran ya yi barazana ga Isra'ila kan Hezbollah

Sakamakon hare-haren da aka kai a Lebanon, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun fitar da gargaɗi mai tsanani ga Amurka da Isra'ila, in ji rahoton BBC.

Hare-haren da Isra'ila ta kai Lebanon a ranar Laraba ya yi silar mutuwat fiye da mutane 200.
Hayaki na tashi daga wani wuri da makamin Iran ya sauka a Kudancin Beirut a ranar 8 ga Afrilu, 2026. Hoto: anwar amro / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta bayyana cewa duk wani hari da aka kai wa Hezbollah, tamkar an kai shi ne ga ƙasar Iran kai tsaye, kuma dakarunsu na shirin daukar matakin da "zai sa abokan gaba su yi da-na-sani".

Gidan talabijin na Iran (IRIB) ya nakalto dakarun na cewa:

"Muna ba Amurka mai saba alkawari da abokiyar huldarta Isra'ila gargaɗi; muddin ba a dakatar da hare-hare kan Lebanon ba, za mu sauke nauyin da ke kanmu wajen mayar da martani mai radadi ga masu tayar da kayar baya a yankin."

Isra’ila ta farmaki motocin agaji a Lebanon

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun IDF na kasar Isra'ila sun kara kai harin ce harin sama a kan motocin agajin gaggawa a Lebanon.

Kara karanta wannan

Ana murna an tsagaita wuta, Trump ya yi maganar da za ta iya harzuka Iran

Bayan mummunan harin da ta kai Kudancin kasar, Isra’ila ta zargi kungiyar Hezbollah da amfani da motocin wajen aikin sojin da suke yi.

Wannan harin dai ya kara dagula yanayin tsaro a yankin, a dai-dai lokacin da ake kokarin hada kan Amurka da Iran su zauna a teburin tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com