Awanni kafin Shiga Zauren Tattaunawa, JD Vance Ya Fallasa Shirin da Amurka Ta Yi Wa Iran
- Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya kama hanyar zuwa birnin Islamabad domin halartar zaman tattaunawa da kasar Iran
- Kafin jirginsa ya tashi daga birnin Washington, JD Vance ya bayyana shirin Amurka da fatan da take a zaman tattaunawar
- A tsakanin ranakun Juma'a da Asabar, 10 ga 11 ga watan Afrilun, 2026 ake sa ran wakilan kasashen biyu za su fara tattaunawa a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington, Amurka - Rahotanni sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya kama hanyar zuwa birnin Islamabad na kasar Pakistan domin fara tattaunawa da Iran.
Haka na zuwa ne bayan Amurka, Isra'ila da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da ya shafe akalla kwanaki 40 ana fafatawa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Amurka da Iran da dab da fara tattaunawa

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Firaministan Isra'ila ya sake dauko rigima bayan dakatar da yakin Iran
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa ana sa ran wakilan Amurka da Iran za su fara tattaunawa kan bukatun kowane bangare domin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Za a fara zaman tattaunawa tsakanin kasashen biyu a yau Juma'a, 10 ga watan Afrilun 2026 a Islamabad da ke Pakistan ko kuma a safiyar gobe Asabar.
Domin isa a kan lokacin, mataimakin shugaban Amurka, JD Vance wanda zai jagoranci tawagar kasar ya bar birnin Washington yau Juma'a tare da kama hanyar zuwa wurin tattaunawar.
Abin da Amurka ke fata daga Iran
A rahoton da NBC News ta tattaro, JD Vance, ya bayyana cewa yana sa ran tattaunawar zaman lafiya da Iran za ta kasance mai kyau kuma ta haifar da 'da mai ido.
Ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da menama labarai jim kadan kafin barin birnin Washington zuwa Pakistan domin halartar ganawar a Islamabad.
JD Vance ya ce:
“Muna sa rai da wannan tattaunawa kuma Ina fatan ganin ta kasance mai kyau.”
Wane shiri Amurka ta yi na tunkarar Iran?
Vance ya kara da cewa Amurka a shirye take ta yi tattaunawa cikin gaskiya idan Iran ma ta nuna irin wannan niyya.

Kara karanta wannan
Abu 1 da Shugaba Trump ya yi da ake tunanin zai zama alheri a tattaunawar Amurka da Iran
“Idan Iran ta nuna gaskiya wajen tattaunawa, mu ma a shirye muke mu mika hannu domin sulhu,” in ji shi.

Source: Getty Images
Sai dai ya yi gargadi cewa idan Iran ta yi kokarin yaudarar Amurka a tattaunawar, ba za su yi mata sassauci ba ko kadan.
“Idan suna son su yaudare mu, za su ga cewa tawagar masu tattaunawa ba za ta karɓi hakan ba. Don haka muna kokarin ganin an yi tattaunawa mai kyau,” in ji shi.
Rawar da ake tunanin JD vance zai taka
A wani rahoton, kun ji cewa an fara yabon matakin Amurka na sanya mataimakin shugaban kasa, JD Vance a cikin wadanda za su jagoranci tattaunawa da Iran.
Tsohuwar jakadiyar Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya, Maleeha Lodhi ta ce Vance gogaggen dan siyasa ne, kuma bai cika son yaki da Iran ba.
A cewar Lodhi, JD Vance na zai zama alheri a wannan tattaunawa da za a yi a birnin Islamabad don cimma yarjejeniya ta karshe
Asali: Legit.ng