Trump Ya Gargadi Netanyahu kan kai Hari Lebanon bayan Tsagaita Wuta
- Amurka ta yi gaggawar gargadin Benjamin Netanyahu kan hare-haren Isra’ila a Lebanon domin kar ya rusa sharadin tsagaitawa da aka yi da Iran
- Shugaba Donald Trump ya bukaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da ya rage yawan hare-haren da ke barazana ga tsagaita wutar
- Hakan na zuwa ne bayan Isra’ila ta ce za ta fara tattaunawa da Lebanon bayan Trump ya aika da saƙo mai ƙarfi ga Netanyahu ta wayar tarho
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya gaya wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya dakatar da munanan hare-haren da ya ke kai wa Lebanon.
Hakan na zuwa ne bayan Faransa, Pakistan wasu kasashen Turai sun bukaci dakatar da hare-haren, inda Iran kuma ta yi barazanar fita daga yarjejeniyar tsagaita wuta.

Source: Getty Images
Lebanon: Trump ya gargadi Netanyahu
A rahoton da Wall Street Journal ta wallafa, Trump ya ce ya tattauna batun Lebanon kai tsaye da Netanyahu, yana nuna cewa Isra’ila za ta dauki mataki kan kai hare-hare.
“Na yi magana da Bibi, kuma zai sassauta lamarin. Ina ganin muna buƙatar mu yi abubuwa cikin natsuwa,”
In ji Trump, yana nufin tattaunawarsa da Firaministan Isra’ila.
Shugaban na Amurka ya ce rage tashin hankali yana da matuƙar muhimmanci domin kiyaye yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi tsakanin Amurka da Iran, yana mai cewa hare-haren Isra’ila a Lebanon sun riga sun fara raguwa.
Daily Sabah ta ce Trump ya kuma nuna kwarin gwiwa sosai kan tsagaita wutar wucin gadin, yana cewa yana ganin yarjejeniyar za ta dore kuma za ta zama tushe ga tattaunawa a gaba.
Magana kan tattaunawa da Iran
A cewarsa, jami’an Iran sun sassauta a tattaunawar sirri, suna nuna shirin amincewa da wasu muhimman sharuda duk da kalamai masu tsauri da suka yi a bainar jama’a.
Tsagaita wutar ta biyo bayan wani lokaci da rikici ya tsananta wanda ya fara da hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Trump ya ce yarjejeniyar ta haɗa da sharuda kamar buɗe mashigar ruwa ta Hormuz, kuma ta dogara ne kan wani shiri mai sharuda10 daga Iran wanda Washington ke ganin zai iya zama ginshiƙi na tattaunawa.

Source: Facebook
Majalisar tsaron Iran ta ce ana sa ran kammala tattaunawar ƙarshe a Islamabad cikin kwanaki 15, yayin da Turkiyya, Pakistan da Masar ke taka rawa wajen sauƙaƙa sadarwa tsakanin ɓangarorin.
Kasar Pakistan ta caccaki Isra'ila
A wani labarin, mun kawo muku cewa Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif ya caccaki yadda Benjamin Netanyahu ke kai hare-hare kasashe da dama.
Asif ya ce Isra'ila ta zama matsala a duniya, inda ya ce kasar na jawo kashe-kashe a yankuna da dama ciki har da Lebanon, Iran da kuma Gaza.
Kalamansa sun zo ne a daidai lokacin da aka sanar da tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka amma Isra'ila ta cigaba da kai hari Lebanon.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

