Putin Ya Sanar da Dakatar da Yakin da Rasha ke Gwabzawa da Ukraine

Putin Ya Sanar da Dakatar da Yakin da Rasha ke Gwabzawa da Ukraine

  • Rahotanni da suka fto daga kasar Rasha sun nuna cewa shugaba Vladimir Putin ya sanar da dakatar da yakin da suke da Ukraine da wasu sa'o'i
  • Hakan na zuwa ne yayin da kasashen ke cigaba da shirin wani muhimmin bikin addini da suka saba, wanda suke ganin yakin zai jawo tsaiko
  • Kafin ayyana tsagaita wutar, kasashen sun yi musayar gawar sojoji sama da 1,000 da aka kashe a yakin da ya dauki sama da shekara hudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Russia - Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sanar da tsagaita wuta na sa'o'i 32 saboda bikin Easter na Orthodox, yayin da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya tabbatar cewa ƙasarsa za ta mutunta wannan yarjejeniya.

Rasha ta ce tsagaita wutar zai fara da karfe 4:00 na yamma agogon Moscow a ranar Asabar, kuma za ta ci gaba har zuwa tsakar dare na ranar Lahadi, wanda ya haɗa da lokacin bikin Easter da ake yi a ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Tun ba a je ko'ina ba, Shugaba Trump ya canza tsarin tattaunawar Amurka da kasar Iran

Vladimir Putin na kasar Rasha
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a ofis. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Putin ya tsayar da yaki da Ukraine

Al-Jazeera ta wallafa cewa yayin sandar da tsagaita wutar, Gwamnatin Putin ta sanar da cewa tana fatan kasar Ukraine za ta mutunta yarjejeniyar.

Sanarwar ta ce:

“Muna fatan cewa ɓangaren Ukraine zai girmama yarjejeniyar,”

Rasha ta ƙara da cewa Ministan tsaro Andrei Belousov ya umarci babban hafsan soji, Valery Gerasimov da su dakatar da ayyukan soja a wannan lokacin.

Sai dai kasar ta ce sojojin Rasha za su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin mayar da martani idan Ukraine da karya yarjejeniyar da aka kulla.

Martanin Ukraine ga kasar Rasha

Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya ce Ukraine ta riga ta gabatar da irin wannan shawara, kuma za ta yi aiki daidai da sharadin da aka kafa.

“Ukraine ta sha bayyana cewa a shirye take ta ɗauki matakai iri ɗaya da Rasha. Mun ba da shawarar tsagaita wuta a lokacin Easter na bana kuma za mu yi aiki da shi,”

Kara karanta wannan

Ana murna an tsagaita wuta, Trump ya yi maganar da za ta iya harzuka Iran

Inji Volodymyr Zelenskyy

Sky News ta rahoto ya kara da cewa:

“Mutane na buƙatar Easter ba tare da barazana ba da kuma duk wani sahihin mataki na kai wa ga zaman lafiya, kuma Rasha na da damar daina kai hare-hare bayan Easter.”
Volodymyr Zelenskyy a wajen wani taro
Volodymyr Zelenskyy yayin magana kan yakin Ukraine da Rasha a Bucha. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai sa’o’i kaɗan bayan sanarwar, gwamnan yankin Dnipropetrovsk ya ce hare-haren makamai daga Rasha sun kashe mutane biyu.

Rasha ta yi musayar gawar sojoji

Rahotanni sun bayyana cewa kafin tsagaita wutar, kasashe Rasha da Ukraine sun yi musayar gawar sojoji sama da 1,000 a tsakaninsu.

Sanarwar gwamnati ta ce:

“Rasha ta miƙa gawar sojojin Ukraine 1,000 ga Kiev a musayar gawar sojojin Rasha 41,”.

Iran da Amurka za su tattauna

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugabannin kasashen Iran da Amurka za su tattauna a kasar Pakistan bayan tsagaita wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Pakistan ce ta shiga ta fita wajen ganin kasashen biyu sun koma teburin sulhu bayan shafe kwanaki suna yaki.

Firaministan Rasha ya bayyana cewa yana fatan tattaunawar da za a yi ta kawo karshen yakin da aka fara a watan Fabrairun 2026 gaba daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng