Tsohon Ministan Iran, Kamal Kharazi Ya Rasu bayan Luguden Wutan Amurka
- Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen Iran ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a harin Amurka da Isra’ila suka kai
- A makon da ya wuce ne Isra'ila da Amurka suka kai hari kan Dr Kamal Kharazi tare da matarsa, ida aka sanar da rasuwarta a lokacin
- Kamal Kharazi ya kasance daya daga cikin manyan masu rike da mukaman gwamnati a Iran, musamman a harkokin diflomasiyyar kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ministan harkokin wajen Iran, Dr Kamal Kharrazi da ya samu raunuka a wani hari da aka kai kan gidansa da ke Tehran ya rasu.
An sanar da cewa ya rasu a daren Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026 kamar yadda matarsa ma ta rasu bayan harin tun farkon makon nan.

Kara karanta wannan
A karon farko, Saudiyya ta yi magana mai muhimmanci da kasar Iran bayan tsagaita wuta

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayananai game da rasuwar Kamal Kharazi ne a wani sako da ofishin Jakadancin Iran a kasar Afrika ta Kudu ya wallafa a X.
Matsayin Kamal Kharazi a Iran
Kharrazi ya kasance babban jigo a harkokin siyasar Iran, yYa riƙe muƙamai masu muhimmanci da dama bayan Juyin Juya Halin Musulunci da aka yi.
Ya yi aiki a matsayin ministan harkokin wajen Iran daga watan Agusta 1997 zuwa Agusta 2005, sannan kuma ya kasance mamba a majalisar tantance muhimman abubuwa na kasar.
Ya kuma kasance shugaban majalisar shawarwari kan harkokin waje, wata hukuma da aka kafa a 2006 wadda ke ba da shawara kai tsaye ga jagororin ƙasar kan manufofin ƙasashen waje da al’amuran duniya.

Source: Twitter
Ayatolla Ali Khamenei da wasu manyan jami’an Iran da kwamandojin soji da dama sun mutu a rikicin da aka fara a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Maganar sulhun Iran da Amurka
Bayan kwana 40 da fara yakin, a halin yanzu, ɓangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta na wucin gadi tare da yarjejeniyar ci gaba da tattaunawa a Islamabad, Pakistan.
Sai dai yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakanin Amurka da Iran tana tangal-tangal, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Kudancin Lebanon, duk da iƙirarin Iran cewa yankin na cikin yarjejeniyar wucin gadi.
Yunkurin kashe Kharazi a baya
A makon da ya gabata, Al-Jazeera ta ruwaito a ranar Alhamis cewa an kai hari ta sama kan gidan Kharrazi da ke Tehran, inda aka ce an kwantar da shi a asibiti cikin mawuyacin hali.
Rahoton ya ce:
“Mun ga abin da ya yi kama da yunƙurin kashe tsohon ministan harkokin wajen, Kamal Kharrazi… Ba mu san dalilin da ya sa aka kai masa hari ba. Ya ji munanan raunuka, kuma matarsa ta mutu,”
Faransa ta yi tir da Isra'ila
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin kasar Faransa karkashin Emmanuel Macron ta yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a Lebanon.
Hakan na zuwa ne bayan yarda da tsagaita wuta da Amurka da Isra'ila ta suka yi a yakin da ya dauki tsawon kwana 40 ana fafatawa.
Shugaban Faransa ya sanar da cewa ya kira Donald Trump ta waya yana jaddada masa bukatar sanya Lebanon a yarjejeniyar da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
