Sulhu Ya Fara Daukar Azama, Isra'ila Ta Sauko game da Matakin Rufe Masallacin Kudus

Sulhu Ya Fara Daukar Azama, Isra'ila Ta Sauko game da Matakin Rufe Masallacin Kudus

  • Hukumomi a kasar Isra'ila sun sake bude Masallacin Kudus da ke Gabashin Kudus bayan kwanaki 40 da aka rufe shi
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa dubban Falasdinawa sun hallara a masallacin domin gudanar da sallar asuba
  • Rahotanni sun nuna kusan mutane 3,000 ne suka shiga harabar masallacin da safe, yayin da aka sassauta takunkumin tsaro da aka sanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Hukumomi a kasar Isra'ila sun sake bude harabar Masallacin Kudus bayan shafe kwanaki da dama a kulle.

An tabbatar da cewa an kulle masallacin na tsawon kwanaki 40 saboda dalilin tashin hankali da ke faruwa a yankin.

Isra'ila ta bude masallacin Kudus ga Musulmi
Musulmai sun taru a masallacin Kudus (Al-Aqsa) a ranar Juma'a ta biyu ta Ramadan. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu.
Source: Getty Images

An sake bude masallacin Kudus

Rahoton Al Jazeera ya tabbatar ya nuna yadda Falasdinawa ke shiga masallacin da safe ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026, kusan mutane 3,000 suka halarci sallar asuba.

Kara karanta wannan

Bayan Iran, gwamnatin Trump ta juyo Najeriya, ta yi gargadi kan tsaro

A baya, an hana shiga gaba daya ko an takaita ga mutane kalilan a wuraren ibada na Kiristoci, Yahudawa da Musulmi bayan barkewar yakin Amurka da Isra’ila da Iran.

Hukumar kula da wuraren addini ta Waqf a Kudus ta tabbatar da cewa za a bude kofofin masallacin ga duk masu ibada tun daga asuba, amma ba ta bayar da karin bayani ba.

Bidiyoyin da suka gabata sun nuna yadda masu aikin sa kai da masu kula da masallacin ke shirya harabar domin karbar masu ibada da gudanar da ibadu.

Hukumomin Isra’ila sun sanar da bude Masallacin Al-Aqsa da kuma Cocin Holy Sepulchre a Kudus a daren ranar Laraba, bayan sababbin umarnin tsaro.

'Yan sanda Isra’ila sun danganta matakin bude wuraren ibada da abin da suka kira “sababbin umarni daga rundunar tsaron cikin gida ta Isra’ila.”

Isra'ila ta bude masallacin Kudus bayan kwanaki 40 a rufe
Frayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Matakan da aka dauka Masallacin Kudus

Sanarwar ta bayyana cewa an kara tsaurara tsaro da girke daruruwan jami’an ‘yan sanda da masu gadin kan iyaka a tsohon birnin Kudus domin kare masu ziyara.

Kudus da wuraren ibadarta sun fuskanci tsauraran matakan tsaro da rufewa akai-akai a cikin makonni shida na rikicin yankin da ya shafi kasashe da dama, cewar Turkiye Today.

Kara karanta wannan

Ana batun, tsagaita wuta, Isra'ila ta saba ka'ida, ta hallaka limamin Musulunci

Takunkumin ya rage armashin bukukuwan Lent, Passover da Ramadan a wuraren ibada masu tsarki ga addinai uku na duniya.

Hukumomi sun hana gudanar da sallar Idi a Masallacin Kudus a wannan shekara, karo na farko tun bayan mamayar Gabashin Kudus da Isra’ila ta yi a 1967.

Sai dai yanzu an dage takunkumin a daidai lokacin da Kiristocin Orthodox ke shirin bikin Easter ranar Lahadi, mako guda bayan na Katolika da Furotesta.

Masallacin Kudus: Kasashen Musulmi sun fusata

Mun ba ku labarin cewa wasu kasashen Musulmi da Larabawa takwas sun soki Israel kan rufe Masallacin Al-Aqsa a Jerusalem yayin watan Ramadan.

Ministocin harkokin wajen kasashen sun ce hana shiga masallacin ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma tsokana ce ga masu ibada.

Sun bukaci gwamnatin Benjamin Netanyahu ta bude wuraren ibada a tsohon birnin Jerusalem a Isra'ila nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.