Mojataba Khamenei Ya Fitar da Zazzafan Sako yayin da Aka Cika Kwana 40 da Kisan Mahaifinsa

Mojataba Khamenei Ya Fitar da Zazzafan Sako yayin da Aka Cika Kwana 40 da Kisan Mahaifinsa

  • Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya fitar da sako ga mutanen kasar yayin da aka tsagaita wuta a yakin da ake yi
  • Mojtaba Khamenei ya fitar da sakon ne ga mutanen Iran yayin da aka cika kwanaki 40 da kashe mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei
  • Sabon jagoran addinin ya bayyana cewa kasar Iran ba ta bukatar yaki da Amurka amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkokinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya fitar da sako yayin da aka tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Amurka da Isra'ila.

Mojataba Khamenei ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta bukatar yaki da Amurka da Isra'ila, amma za ta kare hakkokinta na kasa.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

Mojtaba Khamenei ya ce Iran ba ta son yaki
Mojtaba Khamenei na gaisawa da jama'a a wajen wani taro Hoto: Rouhollah Vahdati
Source: Getty Images

Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton cewa Mojtaba Khamenei ya bayyana hakan ne cikin wani rubutaccen sako a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.

An cika kwanaki 40 da kashe Ali Khamenei

Mojtaba Khamenei ya fitar da sakon ne yayin da ake cika kwanaki 40 da kisan mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei.

Isra'ila da Amurka dai sun kashe Ayatollah Ali Khamenei ne a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Wane sako Mojtaba Khamenei ya fitar?

"Ba mu nemi yaki ba, kuma ba mu bukatar sa. Amma ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba wajen neman hakkokinmu na halal a karkashin kowane irin yanayi, kuma a wannan fanni, muna kallon daukacin dakarun gwagwarmaya a matsayin tsintsiya madaurinki daya."

- Mojtaba Khamenei

A wannan makon ne Iran ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta mai cike da dar-dar na tsawon mako biyu da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Ba boye boye, an ji abin da Saudiyya da wasu kasashe suka yi yayin sulhunta Amurka da Iran

Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta iya kai wa ga tattaunawar zaman lafiya, bayan barazanar ruguza kasar Iran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi.

Mojtaba ya aika sako ga mutanen Iran

Tashar Aljazeera ta ce Mojtaba Khamenei ya shaida wa mutanen Iran cewa kada su "yi tunanin cewa fitowa zanga-zanga a kan tituna ba ta da muhimmanci" duk da sanar da tsagaita wutar da aka yi.

Ayatollah Khamenei ya jaddada cewa kada a amince da tunanin cewa tattaunawa da makiya zai rage bukatar shigar jama'a cikin al'amura.

Mojtaba ya aika sako ga mutanen Iran
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B
Source: Getty Images
"Saboda haka, koda ana tunanin cewa mun shiga matakin daina musayar wuta, hakki ne na kowane dan kasa da ke da ikon fitowa tituna, unguwanni, da masallatai ya kara kaimi wajen shiga zanga-zangar."

- Mojtaba Khamenei

Jagoran ya tabbatar da cewa kukan mutane a kan tituna yana da tasiri a kan tattaunawa.

"Tabbas, muryoyinku a kan tituna suna da tasiri kai tsaye ga tattaunawa, kamar yadda miliyoyin mutanen da ke karuwa a fafutukar 'Shahidan Iran' su ma muhimman abubuwa ne a cikin wannan kokarin."

- Mojtaba Khamenei

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Khamenei yana goyon bayan Hezbollah

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya aika da sako ga Shugaban kungiyar Hezbollah, Naim Qassem.

A cikin sakon na sa ga shugaban Hezbollah, Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da mayar da martani kan hare-haren Amurka da Isra'ila.

Mojtaba ya yaba da jagoranci da jarumta da sadaukarwar mayakan Hezbollah, yana mai kara tabbatar da haɗin kai tsakanin Iran da kungiyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng