Abu 1 da Shugaba Trump Ya Yi da Ake Tunanin Zai Zama Alheri a Tattaunawar Amurka da Iran

Abu 1 da Shugaba Trump Ya Yi da Ake Tunanin Zai Zama Alheri a Tattaunawar Amurka da Iran

  • An fara yabon matakin Amurka na sanya mataimakin shugaban kasa, JD Vance a cikin wadanda za su jagoranci tattaunawa da Iran
  • Tsohuwar jakadiyar Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya, Maleeha Lodhi ta ce Vance gogaggen dan siyasa ne, kuma bai cika son yaki da Iran ba
  • Ta bayyana cewa Mataimakin shugaban Amurka zai zama alheri a wannan tattaunawa da za a yi a birnin Islamabad don cimma yarjejeniya ta karshe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Pakistan - Kasar Amurka ta yi abin da ake ganin yana da kyau kuma zama alheri a tattaunar da za a fara tsakaninta da wakilan Iran a birnin Islamabad.

Tsohuwar jakadiyar Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya, Maleeha Lodhi, ce ta bayyana hakan bayan ganin sunan Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, a cikin wadanda za su halarci zaman.

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin sa hannu a wata takarda a fadar White House Hoto: Joe Riddle
Source: UGC

Tashar Al-Jazeera ta rahoto Lodhi na cewa sanya JD Vance a matsayin jagoran tawagar Amurka zuwa tattaunawar Islamabad mataki ne da ake kallonsa da kyau a Pakistan.

JD Vance zai taka rawa a taron Islamabad

A cewar Lodhi, ana ganin Vance a matsayin wanda ya fi dacewa saboda wasu dalilai da suka hada da bai cika son shiga yaki da Iran ba, kasancewarsa cikakken ɗan siyasa mai kwarewa kuma yana da fahimtar yadda za a cimma matsaya ta sasanci

Ta kwatanta shi da sauran wakilan kasar Amurka kamar Steve Witkoff da Jared Kushner, tana mai cewa Vance ya fi su goge wa a siyasa.

Ta ce:

“‘Yan siyasa sun san yadda za a nemo mafita mai yiwuwa, saboda haka wannan kyakkyawan mataki ne daga gwamnatin Trump.”

Abin da ake sa ran cimmawa a Pakistan

Lodhi ta bayyana cewa babu tabbacin bangarorin biyu, watau Amurka da Iran, za su kai ga cikakkiyar yarjejeniya cikin ‘yan kwanaki kadan, ana ganin zai dauki lokaci.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

Sai dai ta ce abin da ya fi muhimmanci shi ne gina amincewa tsakanin bangarorin, cimma wata fahimta ta gaba daya da sanya tubalin yarjejeniya ta gaba.

JD Vance.
Mataimakin shugaban kasar Amurk, JD Vance yana jawabi a fadar White House Hoto: Jonathan Ernst
Source: Getty Images

Ta kuma nuna cewa a halin yanzu akwai bambanci tsakanin shawarwarin bangarorin biyu, inda Amurka ta gabatar da bukatu 15 yayin da Iran ta gabatar da guda 10.

"Wadannan tsare-tsare da sharudda na karo da juna, amma ana iya tattauna su domin nemo matsaya," in ji Maleeha Lodhi.

A cewarta, bayan tattaunawar da za a yi tsakanin Amurka da Iran a Islamabad, kowane bangare zai koma kasarsa domin neman amincewa daga bisani a ci gaba da tattaunawa kan cikakkun bayanai, cewar Vangaurd.

Iran ta bai wa Amurka zabi guda 2

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Iran ta bukaci Amurka ta zabi daya tsakanin tsagaita wuta da ci gaba da kai wa juna hare-hare ta hannun Isra'ila.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hare-haren da Isra'ila ta sake kai wa kasar Lebanon.

Araghchi ya yi gargadin cewa dole ne Amurka ta zabi daya daga cikin biyu: ci gaba da yaki ta hanyar Isra'ila ko kuma tsagaita bude wuta da nufin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262