Ana Wata ga Wata: Shugaban Iran Ya Fadi Abin da ba Za Su Taba Kyalewa ba

Ana Wata ga Wata: Shugaban Iran Ya Fadi Abin da ba Za Su Taba Kyalewa ba

  • Isra'ila ta kaddamar da hare-hare masu muni a yankuna da dama na Lebanon duk da tsagaita wutar da aka yi
  • Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya fito ya soki Isra'ila kan karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla
  • Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa ci gaba da hare-haren na Isra'ila zai sanya tattaunawa ta zama mara ma'ana

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa hare-haren da Isra’ila take kai wa Lebanon sun saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla da Amurka.

Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa hare-haren za su sanya tattaunawar zaman lafiya ta zama marar ma’ana.

Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Talata, bisa sharudda 10 da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kaddamar domin samar da zaman lafiya.

Sai dai, Isra’ila da Amurka sun nace cewa tsagaita wutar ta shafi hare-hare ne kawai tsakanin Amurka, Isra’ila, da Iran.

Tun daga lokacin, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon.

Me shugaban Iran ya ce kan lamarin?

Shugaban na Iran ya tabbatar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da Lebanon.

"Sake katsalandan ɗin da Isra’ila ta yi a Lebanon babban rashin mutuntawa ce a fili ga yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko. Wannan wata alama ce mai haɗari ta yaudara da rashin sadaukarwa ga yarjejeniyoyin da za a iya ƙullawa."
"Ci gaba da waɗannan ayyukan zai sa tattaunawa ta zama marar ma’ana. Muna cikin shirin ko ta kwana. Iran ba za ta taɓa barin 'yan uwanta maza da mata na Lebanon ba."

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta gano matsala a sharuddan tsagaita wuta, ta shirya koya wa Isra'ila darasi

- Masoud Pezeshkian

Shugaban majalisar Iran ya soki Amurka

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan sharuddan guda 10 ga jama'a ba, shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Ghalibaf, ya bayyana cewa Lebanon wani muhimmin ɓangare ne na yarjejeniyar tsagaita wuta na mako biyu da aka yi da Amurka.

Shugaban kasar Iran ya yi magana kan tsagaita wuta
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ghalibaf a wani rubutu a shafinsa na X ya soki Amurka kan abin da ya kira "maimaita" keta alƙawuran da aka ɗauka. Har ila yau, amincewa da inganta sinadarin uranium ɗin da Iran take yi na ɗaya daga cikin sharudda 10 na shirin zaman lafiyan.

Sai dai, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta yi aiki da Iran ne wajen "haƙowa tare da kwashe" abubuwan nukiliya da aka binne a ƙasar.

Ghalibaf ya kammala da cewa tattaunawa, a daidai lokacin da ake keta alƙawura, "rashin hankali ne."

Iran ta magantu kan sarrafa Uranium

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin Iran ta bayyana cewa tana da hakkin ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Shugaban hukumar kula da harkokin nukiliyar Iran, Mohammed Eslami, ya jaddada cewa kasar Iran ba za ta amince da hana ta sarrafa sinadarin uranium ba.

A cewarsa, bukatar da Amurka ke yi na Iran ta daina sarrafa uranium ba za ta taba karbuwa ba domin hakkinta ne kuma ba za ta yarda a take wannan hakki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng