Kasar Iran na Shirin Ballo Ruwa, Za Ta Jawo Rigima da Amurka kan batun Nukiliya
- Kasar Musulunci ta Iran ta nanata cewa sarrafa sinadarin Uranium da take yi hakkinta ne da babu wanda ya isa ya tauye mata shi
- Shugaban hukumar kula da shirin nukiliyar Iran, Mohammed Eslami ne ya bayyana haka yayin da ake shirin fara tattaunawa a Islamabad
- Tun kafin barkewar rikicin baya-bayan nan da ya shafe fiye da wata guda, Amurka da Iran na gudanar da tattaunawa kan shirin nukiliya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin Musulunci ta kasar Iran ta jaddada cewa tana da hakkin ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium duk da fargabar Amurka cewa tana shirin hada makamin nukiliya ne.
Shugaban hukumar kula da harkokin nukiliyar Iran, Mohammed Eslami, ya jaddada cewa kasar Iran ba za ta amince da hana ta sarrafa sinadarin uranium ba.

Source: Getty Images
Iran za ta hakura da kera makamin nukiliya?

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka
Jaridar Vanguard ta ruwaito Eslami na cewa Iran ba za ta yarda a hana ta sarrafa wannan sinadari ba musamman a tattaunawar zaman lafiya da za ta fara da Amurka.
Mohammed Eslami ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman na tunawa da tsohon jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya gudana yau Alhamis.
Dubbannin mutanen Iran ne suka fito a birnin Tehran domin nuna jimami da tunawa da marigayi Ali Khamenei, wanda ya rasa ransa a yakin Iran da Amurka/Isra'ila, in ji rahoton NBC News.
A cewarsa, bukatar da Amurka ke yi na Iran ta daina sarrafa uranium ba za ta taba karbuwa ba domin hakkinta ne kuma ba za ta yarda a take wannan hakki ba.
Ya ce:
“Wannan buri nena su kawai, kuma wannan buri za a birne shi kowa ya manta da shi, amma Iran ba za ta aminta da shi ba.”
Tun kafin barkewar rikicin baya-bayan nan da ya shafe fiye da wata guda, Amurka da Iran na gudanar da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, wanda ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a duniya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, na kokarin hana Iran mallakar makamin nukiliya. Sai dai Iran ta sha nanata cewa ba ta neman kera makamin nukiliya amma tana da ‘yancin sarrafa uranium domin amfani na zaman lafiya

Source: Getty Images
Shirin tattaunawar Amurka da Iran
Bayan sanar da tsagaita wuta na makonni biyu da Trump ya yi, ana sa ran jami’an Iran da Amurka za su gana a Islamabad a ranar Juma’a domin tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin.
Wannan matsaya ta Iran na nuna cewa har yanzu akwai babbar takaddama tsakanin bangarorin biyu, musamman kan batun nukiliya.
Masana na ganin cewa wannan batu ne mai wahala wajen warware wa, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ko gazawar duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da ake kokarin cimmawa.
Iran ta amince za ta zauna da Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta tabbatar da cewa za ta tura tawagar wakilanta zuwa wurin da aka tanada domin tattaunawa da Amurka da Isra'ila.
A cewar jakadan Iran a Pakistan, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan sharudda 10 da Iran ta gabatar a matsayin hanyar samar da mafita ga rikicin.
Reza Amiri Moghadam ya nuna cewa akwai rashin amincewa a tsakanin ‘yan Iran, musamman saboda zargin cewa Isra’ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Asali: Legit.ng
