Kasar Iran Ta Amince Za Ta Tura Tawaga, Ta Bayyana Abin da Za Ta Gabatar ga Amurka

Kasar Iran Ta Amince Za Ta Tura Tawaga, Ta Bayyana Abin da Za Ta Gabatar ga Amurka

  • Iran ta tabbatar da cewa za ta tura tawagar wakilanta zuwa wurin da aka tanada domin tattaunawa da Amurka da Isra'ila
  • Jakadan Iran a kasar Pakistan, Reza Amiri Moghadam ya bayyana cewa tawagar kasarsa za ta isa birnin Islamabad yau Alhamis
  • Ya nuna cewa akwai rashin amincewa a tsakanin ‘yan Iran, musamman saboda zargin cewa Isra’ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Pakistan - Jakadan kasar Musulunci ta Iran a Pakistan, Reza Amiri Moghadam, ya sanar cewa wata tawaga daga kasarsa za ta isa birnin Islamabad a daren yau Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026.

Moghadam ya ce Iran za ta tura tawaga zuwa Pakistan ne domin tattaunawa kan yadda za a warware rikicin da ke tsakaninta da Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran

Reza Amiri Moghadam.
Jakadan Iran a kasar Pakistan, Reza Amiri Moghadam Hoto: @IranAmbPak
Source: Twitter

Tawagar Iran ta nufi kasar Pakistan

Jakadan ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar yau yayin da aka fara nuna wa juna yatsa tsakanin Iran da Amurka kan ci gaba da kai hare-hare Lebanon.

Iran ta fito fili ta yi Allah wadai da sababbin hare-haren da Isra'ila ta kai kasar Lebanon a jiya Laraba duk da yarjejeniyar da aka yi ta tsagaita wuta.

Hakan dai ya sa aka fara fargabar yiwuwar Iran ta janye daga tattaunawar da aka shirya a Islamabad bayan ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta muddin Isra'ila ta ci gaba da kai farmaki Lebanon.

Sai dai jakadan Iran a Pakistan, Moghadam ya warware wannan fargaba, inda ya ce tawagar Iran za ta isa wurin tattaunawar a yau Alhamis.

Abubuwan da za a tattauna a taron

A cewar jakadan, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan sharudda 10 da Iran ta gabatar a matsayin hanyar samar da mafita ga rikicin.

Kara karanta wannan

Tun ba a je ko'ina ba, Shugaba Trump ya canza tsarin tattaunawar Amurka da kasar Iran

Moghadam ya ce:

“Duk da shakku da ra’ayoyin jama’ar Iran ke da shi sakamakon yadda Isra’ila ke karya yarjejeniyar tsagaita wuta, tawagar Iran za ta isa birnin Islamabad yau domin gudanar da tattaunawa mai muhimmanci bisa sharudda 10 da Iran ta gabatar.”
Jagoran Iran.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei tare da sojoji Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Mutanen kasar Iran sun fusata

Jakadan ya nuna cewa akwai rashin amincewa a tsakanin ‘yan Iran, musamman saboda zargin cewa Isra’ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya, cewar rahoton Reuters.

Wannan shakku na iya shafar yadda tattaunawar za ta gudana, duk da cewa gwamnatin Iran ta nuna aniyarta na ci gaba da neman mafita ta hanyar diflomasiyya.

Sharuddan da ake zargin Amurka ta karya

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya lissafa sharudda uku da yake zargin Amurka ta karya a yarjejeniyar tsagaita wuta.

Wannan zargi dai na zuwa ne kasa da kwana guda bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke yaki a Gabas ta Tsakiya.

Ghalibaf ya bayyana cewa irin wannan hali na kara tabbatar da rashin amincewar da Iran ke yi wa Amurka tun shekaru da dama da suka shige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262