Faransa Ta Sako Netanyahu a Gaba, Ta Kira Trump da Iran kan Harin Isra'ila a Lebabon
- Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da wasu hare-haren da Isra'ila ta kai yankunan kasar Lebanon bayan tsagaita wuta
- Macron ya bayyana cewa hare-haren sun jawo asarar rayuka kuma ya zama wajibi kasar Lebanon ta kasance cikin tsarin dakatar da yakin Iran
- Ya kuma tabbatar da cewa ya yi magana da Shugaba Donald Trump, Shugaban kasar Iran da wasu shugabannin duniya game da dakatar da yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France - Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya fitar da sanarwa game da yakin da aka dakatar na mako biyu tsakanin Iran da Amurka.
Ya kuma yi magana kan manyan hare-hare da Isra'ila ta kai Lebanon da suka yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane bayan tsagaita wuta da aka yi.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Emmanuel Macron ya yi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X bayan tattaunawa da shugabannin duniya.
Martanin Emmanuel Macron kan harin Lebanon
A wani bayani da ya yi, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya yi magana da Shugaban Lebanon, Joseph Aoun, da kuma Firaministan kasar, Nawaf Salam.
Ya ce:
"Na bayyana cikakken goyon bayan Faransa dangane da hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama. Muna Allah-wadai da wadannan hare-hare da kakkausar murya.
Game da shigar da Lebanon cikin yarjejeniyar, Macron ya kara da cewa:
"Wadannan hare-hare na barazana kai tsaye ga dorewar tsagaita wutar da aka cimma kwanan nan. Ya zama dole Lebanon ta kasance cikin wannan tsagaita wuta."
"Na jaddada bukatar kiyaye cikakken ikon Lebanon da kuma kudurin Faransa na tallafa wa kokarin hukumomin kasar wajen kare ‘yancin kanta da aiwatar da shirin kwace makaman kungiyar Hezbollah."

Source: Getty Images
Maganar Faransa kan yakin Iran
Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da cewa ya yi magana shugaban Iran, Massoud Pezeshkian, da kuma shugaban Amurka, Donald Trump kan tsagaitwa wuta da suka yi.
Al-Jazeera ta wallafa cewa ya ce:
"Na shaida musu duka cewa shawarar da suka dauka na amincewa da tsagaita wuta ita ce mafi dacewa."
"Na bayyana fatan cewa za a mutunta tsagaita wutar daga dukkan bangarorin da ke yaki, a dukkan wuraren da ake fafatawa, ciki har da Lebanon.
"Wannan shi ne sharadi mai muhimmanci domin tsagaita wutar ta zama mai inganci kuma mai dorewa."
Macron ya bayyana cewa wannani ne abin da na tattauna da shugabannin Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Lebanon da Iraki.
Faransa ta ba Lebanon motocin yaki
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Faransa ta mika wasu manyan tankokin yaki guda 39 ga gwamnatin kasar Lebanon.
Gwamnatin Emmanuel Macron ta sanar da cewa ta mika motocin ne domin taimakawa Lebanon ta magance barazanar da Isra'ila ke mata.
Rahoto ya nuna cewa Lebanon ta fara fuskantar sababbin hare-haren Isra'ila ne tun farkon watan Maris, 2026 da yakin Iran da Amurka ya fadada zuwa kasar.
Asali: Legit.ng

