Rasha Ta Ce Iran Ta Gwada 'Makamin Nukiliyarta' bayan Tsagaita Wuta

Rasha Ta Ce Iran Ta Gwada 'Makamin Nukiliyarta' bayan Tsagaita Wuta

  • Gwamnatin kasar Rasha ta yi bayani game da tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Iran bayan shafe kwana 40 ana gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Mataimakin kwamitin tsaron Rasha, Dmitry Medvedev ya yi magana game da mashigar Hormuz da aka fara sanar da cewa Iran ta toshe kan kai hari Lebanon
  • A wani sako da ya fitar ga manema labarai, Dmitry Medvedev, ya bayyana babban abin da Iran ke da shi da ya kwatanta da makamin nukiliya a yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rasha - Rahotanni sun nuna cewa kasashe da dama na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Iran.

Mataimakin kwamitin tsaron Rasha, Dmitry Medvedev ya bayyana cewa babu tabbas kan yadda makomar tsagaita wutar za ta kasance yayin da ake shirin tattaunawa a Pakistan.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Iran ba, Trump ya sake barazana kan kwace Greenland

Shugaba Vladimir Putin a ofis
Vladimir Putin zaune a ofishinsa da ke Rasha. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, Medvedev ya yi magana kan karfin da Iran ke da shi, musamman a kan mashigar Hormuz.

Hormuz ne nukiliyar Iran

Mataimakin shugaban kwamitin tsaro, Dmitry Medvedev, ya bayyana a ranar Laraba cewa mashigar Hormuz ne makaman nukiliya na Iran.

Rahotanni sun nuna cewa Dmitry Medvedev ya bayyana cewa Hormuz babban makami ne da Iran za ta yi aiki da shi kuma a ko da yaushe yana nan daram.

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa ya ce:

“Ba a san yadda tsagaita wuta tsakanin Washington da Tehran za ta kaya ba. Amma abu daya ya tabbata — Iran ta gwada makaman nukiliyarta. Wannan shi ne mashigar Hormuz. Karfinsa ba ya karewa,”

Yadda aka tsagaita wuta a yakin

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Talata cewa an cimma tsagaita wuta na mako biyu da Iran, yana mai cewa Tehran ta gabatar da wata shawara mai maki 10 da za a iya aiki da ita domin tattaunawa.

Kara karanta wannan

Faransa ta sako Netanyahu a gaba, ta kira Trump da Iran kan harin Isra'ila a Lebabon

Sanarwar tsagaita wutar ta zo kasa da sa’o’i biyu kafin karewar wa’adin da Trump ya sha tsawaitawa ga Iran domin bude mashigar Hormuz da amincewa da yarjejeniya ko kuma ta fuskanci babban bala'i daga gare shi.

Tashin hankali a yankin ya karu tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare tare a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 1,400 zuwa yanzu.

Yadda mashigar Hormuz ta ke
Yadda mashigar Hormuz ta ratsa ta kasar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila, da kuma wasu kasahen Gabas ta Tsakiya.

Iran da Amurka za su tattauna

A wani labarin, mun kawo muku cewa bayan shiga tsakani, gwamnatocin Amurka da Iran za su yi zama domin shawo kan matsalolin da suka samu.

Firaministan Pakistan ne ya sanar da haka, inda ya bayyana cewa kasashen za su zauna a ranar Juma'a, 10 ga Afrilun 2026 domin tattaunawa.

Hakan ya biyo bayan yarda da tsagaita wuta na mako biyu da aka yi tsakanin kasashen bayan shafe kwana 40 ana yaki da juna a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng