Tun ba a Je Ko'ina ba, Shugaba Trump Ya Canza Tsarin Tattaunawar Amurka da Kasar Iran
- Shugaba Donald Trump ya nuna damuwa game da jerin sharuddan da ake yadawa tare jingina su ga yarjejeniyar tsagaita wuta ta Amurka da Iran
- Sakamakon abin da ya kira karairayin da ake yadawa, Trump ya ce Amurka za ta tattauna kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa a asirce
- Wannan na zuwa ne bayan tsagaita wuta a yakin Amurka/Isra'ila da Iran, bayan shafe sama da wata guda ana musayar wuta a Gabas ta Tsakiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sauya shirinsa kan yadda za su yi nazari kan sharuddan da ke kunshe a yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Musulunci ta Iran.
Hakan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan Trump ya sanar da cewa Amurka ta fara samun daidaito da Iran, kuma sun amince da dakatar da kai wa juna hare-hare na tsawon mako biyu.

Source: Getty Images
Ana yada karya kan sulhun Amurka da Iran
Bayan cimma matsaya kan tsaida yakin, tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa an fara yada sharudda iri daban-daban da ake dangantawa da yarjejeniyar Amurka da Iran.
Wasu daga cikin sharuddan na da ake yadawa suna cikin yarjejeniyar yayin da wasu kuma ana zargin kirkirarsu aka yi.
A wani sako da ya fitar kan wannan lamarin, Shugaba Trump ya fito ne yana mai sukar wasu bayanai na karya da ake jinginawa yarjejeniyar Amurka da Iran.
Sai dai Shugaban na kasar Amurka bai fito fili ya bayyana takamaiman ikirarin da yake nufi da na karya ba, kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.
Matakin da Shugaba Trump ya dauka
“Mutane da dama wadanda ba su da wata alaka da tattaunawar Amurka da Iran suna ta aikewa da dinbin yarjejeniyoyi, jerin sunaye, da wasiku; kuma a mafi yawan lokuta, wadannan mutane ‘yan damfara ne, makaryata, sun ma wuce haka.
“Akwai rukuni guda daya kacal na sharudda masu ma'ana wadanda Amurka za ta iya amfana da su, kuma za mu tattauna su (da Iran) ne a asirce (ba a gaban idon jama'a ba).
“Wadannan sune asalin ka'idoji da sharudda, wadanda suka shiga cikin abubuwan da muka amince da tsagaita bude wuta a kansu. Abu ne mai ma'ana, kuma za a iya kammala shi cikin sauki.”
- Donald Trump.

Source: Facebook
Duk da haka, Shugaba Trump bai lissafo wadannan matakai da ka'idoji da ya kira na gaskiya a yarjejeniyar da Amurka ta cimma da kasar Iran, wanda ya kai ga dakatar da yaki.
Pakistan ta yabi Saudi da wasu kasashe
A wani rahoton, kun ji cewa Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif ya bayyana kasashen da suka ba da goyon baya a kokarin sulhunta Amurka/Isra'ila da Iran.
Shahbaz Sharif ya godewa kasashen China, Saudiyya, Turkiyya, Masar, da Qatar bisa goyon bayan da suka bayar ga tsarin tsagaita bude wuta.
Shugaban ya bayyana cewa wadannan kasashe sun bayar da gagarumin goyon baya mara iyaka wajen cimma matsayar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin da ke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran.
Asali: Legit.ng

