An Yi Barna: Isra'ila Ta Kai Hare Hare Masu Muni a Lebanon
- Dakarun sojojin Isra'ila sun kai hare-hare masu muni kan wasu yankuna da dama a kasar Lebanon
- Hare-haren na Isra'ila sun tafka barna mai girma sa'o'i kadan bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin Amurka da Iran
- Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa hare-haren sun hallaka mutane kusan 100, yayin da wasu daruruwa suka samu raunuka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Beirut, Lebanon - Isra'ila ta kai gagarumin hari a Lebanon sa'o'i kaɗan bayan tsagaita wutar Amurka da Iran.
Hare-haren Isra'ila sun sauka a wasu cunkoson wuraren kasuwanci da na zama a tsakiyar birnin Beirut ba tare da gargaɗi ba.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare a Lebanon a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.
Isra'ila ta kai hare-hare a Lebanon
Isra'ila ta kai hare-haren ne sa'o'i kaɗan bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.
Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da mafi girman harin haɗin gwiwa a faɗin ƙasar Lebanon tun bayan fara wani sabon samamen soja a ƙasar ranar 2 ga Maris.
Hare-haren sun sauka a yankunan Beirut, Bekaa Valley da kuma Kudancin Lebanon.
Tun da farko, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ba ta haɗa da Lebanon ba.
Netanyahu ya bayyana hakan ne a shafin X yayin da yake magana kan batun tsagaita wutar.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa mutane da dama ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da daruruwa suka samu raunuka a hare-haren.
Abin da Isra'ila ta ce kan hare-haren
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce hare-haren sun sauka ne a ababen more rayuwa na Hezbollah.
"Rundunar sjoojin Isra'ila ta gudanar da "wani samamen ba-zata kan daruruwan ’yan ta'addan Hezbollah a cibiyoyin ba da umarni a faɗin Lebanon."
"Wannan shi ne mafi girman farmaki da aka kai wa Hezbollah tun bayan samamen 'Operation Beepers'."
"Cikin mintuna 10 kuma a yankuna da dama a lokaci guda sojojin Isra'ila sun kammala mafi girman harin haɗin gwiwa da ya sauka a fiye da cibiyoyin ba da umarni na Hezbollah 100 da wuraren soja."
- Israel Katz

Source: Getty Images
Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane
Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa aƙalla mutane 89 ne aka kashe, yayin da fiye da 700 suka ji rauni a hare-haren da Isra'ila ta kai a faɗin Lebanon a yau.
Hare-haren saman na Isra'ila sun kashe fiye da mutane 1,530 a Lebanon tun ranar 2 ga Maris, ciki har da mata fiye da 100 da yara 130, sannan fiye da mutane miliyan 1.2 sun rasa muhallansu.
Isra'ila ta kashe limami a Lebanon
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila ta kai wani hari a Kudancin Lebanon wadanda suka jawo asarar rayuka.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadin mutuwar ‘yan mata uku kanana da kuma wani babban limamin Musulunci.
Harin na rundunar sojojin Isra'ila ya kara yawan fararen hula da ke rasa rayukansu a Kudancin Lebanon.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

