Yaƙi bai Ƙare ba: Iran Ta Ƙaddamar da Sababbin Hare Hare kan Saudiyya da Ƙasashe 3

Yaƙi bai Ƙare ba: Iran Ta Ƙaddamar da Sababbin Hare Hare kan Saudiyya da Ƙasashe 3

  • Kasashen Saudiyya, UAE, Kuwait, da Bahrain sun sanar da kakkabo makamai masu linzami da jirage marasa matuka da Iran ta harba yau
  • Harin ya janyo gobara a matatar iskar gas ta Habshan a Abu Dhabi da kuma lalata manyan tashoshin wutar lantarki a kudancin Kuwait
  • Gidan talabijin na Iran ya tabbatar da kai harin, yana mai cewa martani ne kan harin da aka kai wa matatun man ƙasar a safiyar Larabar nan

Dubai - Sa'o'i kaɗan bayan sanarwar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, yankin tekun fasha ya girgiza da wasu sababbin hare-hare a yau Laraba, 8 ga Afrilu, 2026.

Ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Kuwait, da Bahrain sun tabbatar da cewa tsarin kariyarsu ya fafata da makamai masu linzami da jirage marasa matuka da aka harba daga Iran.

Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan Saudiyya da kasashe 3 a Gulf.
Hayaki ya tashi sama bayan Iran ta farmaki hedikwatar sojojin Amurka na Navyâs da ke Manama, a Bahrain. Hoto: Stringer/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

An kai hare hare Dubai, Kuwait

Ma'aikatar tsaron UAE ta bayyana cewa dakarunsu sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami nau'in ballistic da cruise gami da jirage marasa matuka, in ji rahoton Aljazeera.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan asarar da Amurka ta yi yayin yaki a Gabas ta Tsakiya

Sai dai kuma, ɓarnar tarkacen makaman da aka kakkabo ta janyo tashin gobara a matatar iskar gas ta Habshan dake Abu Dhabi, sannan mutane uku sun ji rauni, ciki har da ɗan ƙasar Indiya ɗaya.

Ita ma rundunar sojin ƙasar Kuwait ta sanar da cewa ta fuskanci farmakin jirage marasa matuka kusan guda 28 tun daga ƙarfe 8:00 na safe.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin jiragen sun yi nasarar lallata tashoshin samar da wutar lantarki, matatun mai, da wuraren tace ruwan sha a kudancin ƙasar, lamarin da ya janyo babbar illa ga ababen more rayuwa.

Iran ta tabbatar da kai hare haren

A ƙasar Bahrain ma, an ji ƙarar fashe-fashe a babban birnin ƙasar, Manama, inda tarkacen jiragen da aka kakkabo ya janyo raunuka ga mutane biyu tare da lalata gidaje a yankin Sitra.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta tabbatar da cewa jami'an kashe gobara sun shawo kan wutar da ta tashi a wani babban ginin makamashi da dakarun Iran suka yi niyyar ruguzawa, in ji rahoton Saudi Gazette.

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya tabbatar da kai waɗannan hare-hare, inda ya bayyana cewa dakarunsu sun ƙaddamar da su ne a matsayin martani kan harin bam da aka kai wa matatun man Iran a safiyar yau Laraba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

A Kuwait, Iran ta farmaki tashoshin samar da wutar lantarki, matatun mai, da wuraren tace ruwan sha a kudancin ƙasar Kuwait.
Motoci na wucewa a hanyar da ake iya hango hayaki daga wani yanki na ofishin jakadancin Amurka a Kuwait da Iran ta farmaka. Hoto: AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Saudiyya ta kakkabo jiragen Iran 9

Wannan ikirari na Iran ya nuna yadda yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka sanar take fuskantar ƙalubale sosai tun kafin ta fara aiki yau.

Daga bisani, ma'aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ma ta sanar ta shafinta na X cewa ta yi nasarar kakkabo wasu jirage marasa matuka tara da suka shigo sararin samaniyar ƙasar a cikin sa'o'in da suka gabata.

Duk da cewa ana kan tattaunawar diflomasiyya, akwai yiwuwar za a ci gaba da fuskantar musayar hare-hare a kasashen Gabas ta Tsakiya, kamar yadda The Times of India ta ruwaito a baya.

Iran ta amince da tsagaita wuta da Amurka

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ministan wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar za su dakatar da duk wani harin kare-kai kan Amurka da Isra'ila.

Majalisar ƙolin tsaron ƙasa ta Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "nasara ga al'ummar Iran" tare da gargaɗin Amurka kan sake yin wani kuskuren.

Iran ta yi iƙirarin cewa Amurka ta amince da haƙƙinta na tace sinadarin nukiliya a matsayin wani ɓangare na tattaunawar tsagaita wuta da za a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com