Bayan Yakin Iran, Kim Jong Un Ya Harba Manyan Makamai Masu Linzami
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Koriya ta Arewa karkashin shugaba Kim Jong Un ta harba makamai masu linzami wani yanki kusa da Koriya ta Kudu
- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban Koriya ta Kudu ya yi magana kan wani sameme da jiragen kasar shi su ka kai yankin Koriya ta Arewa
- Makaman da aka harba sun dauki hankalin kasashen duniya, musamma lura da cewa lamarin ya biyo bayan tsagaita wuta da aka yi tsakanin Iran da Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
North Korea - Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami masu gajeren zango sau biyu a ranar Laraba, kamar yadda sojojin Koriya ta Kudu suka bayyana.
Hakan na zuwa ne bayan sun bayar da rahoton cewa an harba wani “abu da ba a tantance ba” daga yankin Pyongyang a ranar da ta gabata.

Source: Getty Images
Alakar Koriya ta Arewa da ta Kudu
Tashar France 24 ta wallafa cewa Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, ya yi kokarin gyara alaka da Koriya ta Arewa tun bayan hawansa mulki a bara.
A ranar Litinin, Seoul ta nuna nadama kan kutsen jiragen sama marasa matuka da suka shiga Koriya ta Arewa a watan Janairun 2026, inda Lee ya bayyana hakan a matsayin “rashin tunani,” yana mai cewa wasu jami’an gwamnati na da hannu a lamarin.
Sai dai masana sun ce harba makaman, wanda shi ne na biyar da aka yi a bana, na nuna yadda Koriya ta Arewa ke kin amincewa da kokarin zaman lafiya daga Koriya ta Kudu.
An harba makamai Koriya ta Kudu
Sojojin Koriya ta Kudu sun ce da safiyar Laraba sun gano wani “abu da ba a tantance ba” da aka harba daga yankin babban birnin Koriya ta Arewa a ranar da ta gabata.
Kimanin awa guda bayan haka, sojojin sun ce sun sake gano “makamai masu linzami da dama da ba a tantance ba” da aka harba da safe daga yankin Wonsan na Koriya ta Arewa.
A cikin sanarwa daban-daban, sojojin sun ce makaman na gajeren zango ne, an harba su da misalin karfe 8:50 na safe, kuma sun yi tafiyar kusan kilomita 240.

Source: Getty Images
An harba daya makamin da shi ma aka ce na gajeren zango ne da misalin karfe 2:20 na rana, inda ya yi tafiyar sama da kilomita 700.
Karin bayani kan harba makamin
Times of India ta wallafa cewa hukumar kula da gabar tekun Japan ta ce an harba wani “abu da ake zargin makami mai linzami ne” daga Koriya ta Arewa, tana gargadin jiragen ruwa da su kasance cikin shiri.
Ofishin tsaron kasa na Koriya ta Kudu a fadar shugaban kasa ya gudanar da taron gaggawa, inda ya bukaci Pyongyang da ta dakatar da irin wadannan matakan tada hankali nan take.
Iran da Amurka za su tattauna
A wani labarin, mun kawo muku cewa kasashen Amurka da Iran za su zauna a teburin sulhu bayan tsagaita wutar mako biyu da suka yi.
Firaministan Pakistan ya sanar da cewa wakilan kasashen za su hadu a kasar shi a ranar Juma'a, 10 ga watan Afrilun 2026 domin tattaunawa.
Ya bayyana cewa yana fatan zaman da za a yi ya kawo karshen matsala da sabani tsakanin kasashen biyu domin wanzar da zaman lafiya a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


