Yakin Iran: Amurka Ta Yi Gargadi kan Aikin Hajjin 2026

Yakin Iran: Amurka Ta Yi Gargadi kan Aikin Hajjin 2026

  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta shawarci ‘yan kasarta su sake nazari kan aikin Hajjin bana na 2026 saboda yakin Iran
  • Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya ne ya fitar da sanarwar a ranar Talata
  • Saudiyya na cikin kasashen da ke da sansanin sojojin Amurka, kuma Iran ta kai musu jerin hare-hare bayan yakin da aka fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudiyya - Ofishin Jakadancin Amurka a kasar Saudiyya ya shawarci ‘yan kasarsa da su sake nazarin yin aikin Hajjin bana sakamakon tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i kaɗan bayan Donald Trump ya yi barazanar kai mummunan hari Iran kafin tsagaita wuta da Pakistan ta jagoranta.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da sanarwa da Amurka ta yarda ta tsagaita wuta da kasar Musulunci

Musulmai na ibada a dakin Ka'aba
Yadda mahajjata ke dawafi a dakin Ka'aba. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Amurka kan Hajjin bana

A wani sako da ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya ya wallafa, ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da kare 'yan kasar a duk inda suke a duniya.

Sanarwar ta ce:

“Bisa ga sanarwar ma'aikatar tafiye-tafiye ta Saudiyya, da kuma halin tsaro da ke gudana tare da katsewar zirga-zirga lokaci-lokaci, muna ba da shawarar a sake tunanin halartar Hajjin bana,”

Anadolu Agency ta rahoto ta kara da cewa:

“Daga ranar 18 ga Afrilu, duk wanda zai shiga Makka dole ne ya gabatar da takardar izinin aikin Hajji, katin zama da aka bayar daga Makka, ko takardar izinin aiki a Makka. Dole sauran wadanda aka ba biza su bar Makka kafin ranar 18 ga Afrilu.”

Rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya

Tashin hankali a yankin ya ci gaba tun bayan da Isra’ila da Amurka suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila, Jordan, Iraki da kasashen yankin Gulf da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa yakin ya haddasa asarar rayuka da lalacewar abubuwan more rayuwa tare da rikita kasuwannin duniya da zirga-zirgar jiragen sama.

Sai dai a ranar Talata, 7 ga Afrilun 2026 an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu sakamakon shiga tsakani da kasar Pakistan ta yi.

Hajjin 2026 da sharudan shiga Makka

Bisa ga sanarwar hukumomin kasar Saudiyya, an sake jaddada cewa dole masu zuwa Hajji su samu izini da biza ta hanyar manhajar Nusuk da kasar ta tanada.

An sanar da cewa duk wanda ya yi kokarin shiga Makka ba tare da wadannan takardu ba za a hana shi shiga, kuma yana iya fuskantar tara, dauri ko kuma korar sa daga kasar.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka yana yi wa Amurkawa bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ranar 3 ga Afrilu 2026 ce ranar karshe da aka ba da damar shiga Saudiyya da bizar Umrah, yayin da dole masu wannan biza su fita kafin 18 ga Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

An rasa rai, yan sanda sun jikkata da aka farmaki ofishin jakadancin Isra'ila

Za a ci gaba da aiwatar da wadannan matakai har zuwa tsakiyar watan Yunin 2026 tare da shawartar jama’a su rika bibiyar sababbin bayanai daga hukumomin Saudiyya.

Ana maganar tsige Trump a Amurka

A wani labarin, mun rahoto muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara fuskantar barazanar siyasa kan yakin da ya yi a Iran.

Wata 'yar majalisar kasar, Ilhan Omar ta yi kira da a tsige shugaba Donald Trump saboda barazanar aikata laifuffukan yaki da ya yi.

Ilhan Omar ta yi kira ga Shugaban Majalisar dokokin kasar da ya dawo da zaman da suke domin tattauna batun tsige shugaba Trump.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng