Shirin Tsagaita Wuta Tsakanin Iran, Amurka Ya Kawo Gagarumin Sauyi a Duniya

Shirin Tsagaita Wuta Tsakanin Iran, Amurka Ya Kawo Gagarumin Sauyi a Duniya

  • Farashin mai ya sauya a kasuwar duniya bayan Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na tsawon makonni biyu
  • Kasuwannin hannayen jari sun tashi a kasashen Asiya yayin da yarjejeniyar ta kawo saukin tashin hankali
  • Duk da tsagaita wutar, masana sun ce gyaran lalacewar ababen more rayuwa da samar da mai zai dauki lokaci mai tsawo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai ya fadi matuka bayan Amurka da Iran sun cimma yarjejeniya ta tsagaita wuta a yakin da ake yi.

Hakan ya biyo bayan amincewa da tsagaita wuta na wucin gadi na makonni biyu, wanda ya hada da bude mashigar ruwa ta Hormuz.

Farashin mai ya fadi daga fara maganar tsagaita a Gabas ta Tsagaita
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei, Shugaba Donald Trump na Amurka da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Farashin Brent crude ya sauka da kusan kashi 13 zuwa $94.80 a kowace ganga, kamar yadda rahoton BBC ya ce.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da sanarwa da Amurka ta yarda ta tsagaita wuta da kasar Musulunci

Iran/Isra'ila: An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya amince da dakatar da hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu, amma bisa sharadin Iran ta bude mashigar Hormuz gaba daya cikin aminci.

Shi ma Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Tehran za ta amince da tsagaita wuta idan aka dakatar da kai mata hare-hare, yana mai cewa zirga-zirgar jiragen ruwa za ta yiwu cikin aminci.

Masana sun ce duk da tsagaita wutar, ana sa ran farashin makamashi zai ci gaba da sauyawa saboda rashin tabbas, yayin da sake dawo da cikakken samar da mai zai bukaci lokaci mai tsawo.

Sun kara da cewa lalacewar da aka yi wa cibiyoyin makamashi a yankin na iya daukar watanni ko ma shekaru kafin a gyara, tare da kashe kudade masu yawa, cewar The Guardian.

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Yadda farashin mai ya fadi a duniya

Majiyoyi sun na Amurka ya ragu da fiye da kashi 15 zuwa $95.75, duk da haka, farashin har yanzu ya fi yadda yake kafin rikicin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Rikicin ya haddasa tashin farashin makamashi bayan Iran ta yi barazanar kai hari kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz domin mayar da martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila, lamarin da ya janyo tangarda a samar da mai da gas daga Gabas ta Tsakiya.

A sakamakon yarjejeniyar, kasuwannin hannayen jari a yankin Asia sun samu karuwa, inda Nikkei 225 na Japan ya tashi da kashi 5, Kospi na Koriya ta Kudu da kusan kashi 6, Hang Seng na Hong Kong da kashi 2.8, yayin da ASX 200 na Australia ya karu da kashi 2.7.

Kalaman Trump ya sauya farashin mai

Kun ji cewa kasuwannin duniya sun fara ganin sauki ta fuskar farashin danyen mai biyo bayan saukar da ya yi.

Farashin danyen man ya kai farashi mafi kololuwa da aka taba gani a duniya tun watan Yulin shekarar 2026 da muke ciki.

Sai dai, bayan barazanar Shugaba Donald Trump da matakin da Ministocin kasashen Turai suka dauka, farashin danyen man ya fara sauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.