Tun ba a Je ko ina ba, Netanyahu Ya Rusa Sharadin Yarjejeniyar Iran da Amurka

Tun ba a Je ko ina ba, Netanyahu Ya Rusa Sharadin Yarjejeniyar Iran da Amurka

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan tsarin tsagaita wuta da Amurka da Isra'ila suka amince da shi
  • A cikin sharuda 10 da Iran ta mika wa shugaban Amurka, Donald Trump kuma ya amince da su akwai daina kai hari Lebanon
  • Sai dai a yanzu haka, Benjamin Netanyahu ya fito ya ce babu maganar daina kai hari Lebanon a cikin yarjejeniyar da aka yi

Isra'ila - Bayan 'yan sa'o'i, an fara hararo matsala game da yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu da aka yi tsakanin Amurka da Iran.

Benjamin Netanyahu ya ce tsagaita wutar Amurka da Iran ba ta shafi Lebanon ba duk da an ambaci haka a cikin yarjejeniyar da Donald Trump ya amince da ita.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a wajen taro a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta gano cewa Netanyahu ya bayyana haka ne a wani sako da Times of Israel ta wallafa jim kadan bayan Amurka da Iran sun cimma matsaya.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Sharadin da Netanyahu ya rusa

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu tsakanin Amurka da Iran ba ta hada da kasar Lebanon ba.

Ofishinsa ya ce Isra’ila na goyon bayan matakin da Amurka ta dauka na dakatar da hare-hare kan Iran na wucin gadi, amma ya jaddada cewa tsagaita wutar ba ta shafi ayyukan sojin Isra’ila a Lebanon ba.

Netanyahu ya ce Isra’ila na goyon bayan kokarin Shugaban Amurka Donald Trump na tabbatar da cewa Iran ba ta zama barazanar nukiliya, makamai masu linzami ga Amurka, Isra’ila da sauran kasashen yankin ba.

Magana kan tattaunawa a Pakistan

Ya kuma bayyana cewa Amurka ta tabbatar wa Isra’ila da kudurinta na cimma wadannan manufofi a tattaunawar da za a fara a Islamabad, babban birnin Pakistan.

Dama dai Pakistan, Masar da wasu ƙasashen Musulmi ne suka shiga suka fita domin ganin an dakatar da yakin da ya shafi tattalin arzikin duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Trump ya dauki matsaya bayan Iran ta yi watsi da tsagaita wuta

An ambaci Lebanon a yarjejeniyar

Sai dai wannan matsaya ta Isra’ila ta saba da abin da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya fada, wanda ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar ta shafi dukkan bangarorin rikicin ciki har da Lebanon.

Shugaba Donald Trump da kansa ya sanar da cewa ya karbi sharuda 10 da Iran ta kafa ta hannun Pakistan kuma akwai maganar daina kai hari Lebanon a ciki.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin wani bayani ga Amurkawa. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Yadda Lebanon ta shiga yakin Iran

Al-Jazeera ta rahoto cewa Lebanon ta shiga cikin rikicin ne tun ranar 2 ga Maris, 2026 bayan kungiyar Hezbollah da ke da alaka da Iran ta fara kai hare-hare kan Isra’ila, lamarin da ya janyo martanin sojojin Isra’ila a cikin kasar.

Duk da tsagaita wutar tsakanin Amurka da Iran, Isra’ila ta nuna cewa za ta ci gaba da kai hari Lebanon, wanda ke nufin rikicin a yankin na iya ci gaba duk da kokarin sulhu da ake yi.

Isra'ila ta kai hari kan Yahudawa

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi magana da kasar Iran ta farmaki muhimmin wuri a Isra'ila

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu hare-haren da Isra'ila ta kai birnin Tehran na Iran ya sauka kan Yahudawa 'yan uwansu.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya ruguza wani babban wajen ibadar da Yahudawa ke taruwa lokaci bayan lokaci domin bukukuwan addini.

Bayanai sun tabbatar da cewa Yahudanci na cikin addinan da aka amince da su a Iran duk da cewa wasu Yahudawa sun bar kasar tun bayan juyin juya hali da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng