'Ba Haka Muka So ba," A Karon Farko, Isra'ila Ta Yi Nadama bayan Kai Hari Iran
- Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana nadamar lalata majami'ar Rafi-Nia dake Tehran yayin wani harin sama da aka kai daren jiya
- Isra'ila ta harba makami don ya fada kan hedikwatar gaggawa ta 'Khatam al-Anbiya', a yunkurin kakkabe wani babban kwamandan IRGC
- Sai dai an samu kuskure, inda makamin ya daki Rafi-Nia, daya daga cikin mahimman wuraren da Yahudawa ke gudanar da bauta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila – Dakarun sojin Isra’ila (IDF) a yau Talata, 7 ga Afrilu, 2026, sun bayyana nadama kan barnar da ta yi wa wata majami’ar Yahudawa dake Tehran a harin sama da suka kai cikin dare.
Wata sanarwa da IDF ta fitar, ta nuna cewa dakarun sojojin sun kai harin ne da nufin kakkabe wani babban jami'in sojin Iran a hedikwatar tsaro ta 'Khatam al-Anbiya.'

Kara karanta wannan
Kasar Musulunci ta yi rashi: Isra'ila ta kashe shugaban hukumar leken asirin Iran

Source: Getty Images
Isra'ila ta yi nadamar kai hari Iran
Kafar watsa labaran The Wall Street Journal, ta ruwaito sanarwar dakarun sojojin tana cewa:
"IDF na nadamar lalacewar majami'ar kuma tana jaddada cewa ta kai harin ne da nufin kakkabe wani babban jami'in soja, ba wai an tsara shi don farmakar wurin ibadar ba."
Tun da safiyar Talata ne kafofin yada labaran Iran suka ruwaito cewa majami'ar Rafi-Nia, daya daga cikin shahararrun wuraren ibadar yahudawa dake tsakiyar birnin Tehran, ta ruguje baki daya sakamakon harin Isra'ila.
Wannan babban gini yana kusa da wuraren da Isra'ila ke zargin ana gudanar da harkokin soji na sirri, wanda hakan ne dalilin kai harin.
Jami'ar Yahudawa ta rushe a harin Isra'ila
Duk da cewa Isra'ila ta ce ba ta da nufin kai hari kan wurin ibadar, rugujewar majami'ar ta sake rura wutar korafi kan yadda ake kai hare-hare a yankunan da fararen hula ke rayuwa.

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
Addinin Yahudanci na daga cikin addinai da doka ta amince da su a Iran, kuma kasar na da al’ummar Yahudawa, duk da cewa da dama sun bar kasar bayan juyin juya halin 1979.
Babu cikakken kididdiga a hukumance da aka fitar, amma ana hasashen akwai dubban Yahudawa da ke zaune a Iran har yanzu.
An bayyana majami’ar a matsayin daya daga cikin muhimman wuraren da Yahudawan Khorasan ke haduwa da gudanar da bukukuwa, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Source: Getty Images
Bayani kan hedikwatar 'Khatam al-Anbiya'
Hedikwatar 'Khatam al-Anbiya' tana daya daga cikin mahimman wuraren gudanar da ayyukan gaggawa da tsaro na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC).
Isra'ila na kallon wannan cibiya a matsayin inda ake tsarawa da kuma ba da umarnin harba makaman linzami da jirage marasa matuka, a cewar rahoton Arab News.
A halin yanzu, gwamnatin Iran ba ta yi karin bayani kan matsayin kwamandan da aka kai harin don shi ba, yayin da duniya ke zuba ido kan martanin da Tehran za ta mayar.
Yahudawa sun rikice bayan harin Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumomin kasar Yahudawa watau Isra'ila sun bayyana wasu daga cikin barnar da hare-haren Iran suka yi wa mutane a kusa da Tel Aviv.

Kara karanta wannan
Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili
Ma'aikatan lafiya da ke bada agajin gaggawa a Isra'ila sun ce akalla mutane 14 suka samu rauni a harin makamin Iran a yankin Bnei Brak.'
Daga cikin wadanda suka samu rauni har da yarinya yar shekara 11 kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayyana.
Asali: Legit.ng