Netanyahu Ya Sake Dauko Batun Muzgunawa Kiristoci a Najeriya

Netanyahu Ya Sake Dauko Batun Muzgunawa Kiristoci a Najeriya

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya aika da sakon Easter ga al'ummar Kiristoci a fadin duniya
  • Benjamin Netanyahu ya nuna damuwa kan cewa Kiristoci na fuskantar muzgunawa a Najeriya da wasu kasashe na duniya
  • Firaministan na Isra'ila ya nuna cewa kasarsa kawai ba ta tsangwamar Kiristoci a yankin Gabas ta Tsakiya

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan abin da ya kira muzgunawa Kiristoci a Najeriya.

Netanyahu ya sake yin Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin tsangwama da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya.

Netanyahu ya ce ana muzgunawa Kiristoci a Najeriya
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙon Easter da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 5 ga watan Afirilun 2026.

Benjamin Netanyahu ya taya Kiristoci murna

Kara karanta wannan

Kasashen Afirka 3 da kasar Isra’ila ta taɓa kai masu farmaki a baya

Netanyahu ya aika da gaisuwa ga Kiristoci a Isra'ila, Amurka, da ma faɗin duniya, inda ya yi musu fatan murnar bikin cikin farin ciki.

Ya bayyana cewa Kiristoci suna fuskantar tsangwama a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya, Siriya, Lebanon, da Turkiyya, amma ya jaddada cewa Isra'ila ce kaɗai ƙasa a Gabas ta Tsakiya inda ake kare al'ummar Kirista kuma adadinsu ke ci gaba da ƙaruwa.

Isra'ila na kare 'yancin addini

Shugaban na Isra'ila ya kuma yi magana kan tashe-tashen hankula da ake yi a yankin, inda ya lura cewa duk da barazanar tsaro da harbo makamai masu linzami da ake yi wa birnin Jerusalem, Isra'ila ta ci gaba da sadaukar da kai wajen kare ’yancin yin addini ga dukkan addinai, musamman a lokacin bikin Easter.

A cewarsa, ƙasar ta tsaya tsayin daka a ƙoƙarinta na kare rayuka, kiyaye ’yanci, da tabbatar da cewa mutane na dukkan addinai za su iya yin addininsu ba tare da tsoro ba.

Netanyahu ya ƙara bayyana fatan cewa lokacin Easter zai kawo sabuntawa da karuwar imani ga Kiristoci a duk faɗin duniya.

Kara karanta wannan

Kwan gaba kwan bayan Donald Trump a yakin Amurka da Iran

Netanyahu ya ce Isra'ila na kare 'yancin addini
Netanyahu da mukarrabansa gwamnatinsa a wajen taro da Kiristoci a Amurka Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Netanyahu ya ce ana tsangwamar Kiristoci

"Ga abokanmu Kiristoci a Isra'ila, Amurka, da ma fadin duniya, muna muku fatan Easter mai albarka da farin ciki."
“Ana tsangwamar Kiristoci a faɗin Gabas ta Tsakiya, a Siriya, Lebanon, Najeriya, Turkiyya, da ma wasu wuraren. Amma a yankinmu, Isra'ila ce kaɗai ke kare al'ummar mu na Kirista, waɗanda ke ƙaruwa kuma suke samun ci gaba."
“A wannan ƙasa inda labarin ya fara, yayin da ake harba makamai masu linzami a babban birninmu, birni mai tsarki na Jerusalem, kuma yayin da Amurka da Isra'ila suka tsaya tsayin daka kan gwamnatin Iran da wakilanta na ta'addanci, mun ci gaba da tsayin daka wajen kare 'yancin yin ibada ga dukkan addinai, musamman a wannan lokaci mai tsarki."
“Ko a lokacin da ake harbe-harbe, sadaukarwarmu ba za ta girgiza ba, don kare rai, kiyaye 'yanci, da tabbatar da cewa kowane mai imani zai iya yin addu'a cikin kwanciyar hankali."

Kara karanta wannan

Isra'ila ta bar boye boye, ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata a yaki da Iran

- Benjamin Netanyahu

Isra'ila ta farmaki wurin bautar Yahudawa

A wani labari kuma, kun ji cewa wani harin da Isra'ila ta kai a Jamhuriyar Musulunci ta Iran,\ ya yi barna a wajen bautar Yahudawa.

Hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila sun lalata wata majami’ar Yahudawa gaba daya a birnin Tehran, babban birnin Iran.

An bayyana majami’ar a matsayin daya daga cikin muhimman wuraren da Yahudawan Khorasan ke haduwa da gudanar da bukukuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng