Pakistan Ta Tura Sako ana cikin Musayar Wuta, Ta Gabatar da Matakai 2 ga Amurka da Iran

Pakistan Ta Tura Sako ana cikin Musayar Wuta, Ta Gabatar da Matakai 2 ga Amurka da Iran

  • Gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa ta karbi daftarin yarjejeniyar da tsagaita wuta mai kunshe da matakai biyu daga kasar Pakistan
  • Rahotanni sun nuna cewa Pakistan ta mika wannan daftari, wanda ya nemi tsagaita wuta nan take da kuma bude mshigar ruwa ta Hormuz
  • Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce a yanzu ta maida hankali ne kan tsaron kasarta sakamakon karuwar hare-hare daga Amurka da Isra'ila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Pakistan - Kasar Pakistan ta gabatar da matakai biyu na yarjejeniya da nufin kawo karshen yakin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, da kuma sake bude mashigar ruwa ta Hormuz.

Wannan na zuwa ne yayin da masu shiga tsakani ke kokarin ganin an tsagaita wuta a yakin da ya barke tun ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Ba boye boye: Iran ta bayyana matsayarta kan tsagaita wuta tsakaninta da Amurka

Mojtana da Trump.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtana Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu, @DonaldTrump
Source: Getty Images

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bangarorin sun karbi daftarin yarjejeniyar kuma sun fara nazari kan wannan tsari da kasar Pakistan ta gabatar.

Yunkurin Diflomasiyyar kasar Pakistan

A safiyar yau Litinin, Esmaeil Baghaei, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, ya tabbatar da cewa akwai kokarin diflomasiyya da Pakistan ke yi don dakatar da yakin.

Sai dai Baghaei ya kara da cewa Iran ta fi mayar da hankali ne kan tsaron kasarta a daidai lokacin da take fuskantar sababbin hare-hare daga Amurka da Isra'ila.

A ranar Litinin din nan, an kai hari kan wata babbar jami'a a Tehran da kuma masana'antar tace man fetur ta South Pars da ke Asaluyeh, inda aka kashe akalla mutane 34 a Iran.

Matakai biyu da Pakistan ta gabatar

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Amurka, Iran, da masu shiga tsakani sun fara tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a bangare na "yarjejeniyar mai kunshe da matakai biyu" wadda za ta iya kaiwa ga kawo karshen yakin baki daya.

Kara karanta wannan

Ana sabon shirin kawo karshen yakin Iran, ana son tsagaita wuta na wasu kwanaki

Majiyar ta kara da cewa babban hafsan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ya tattauna da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, wakili na musamman, Steve Witkoff, da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi a "tsawon daren jiya".

Majiyar ta ce, "ana bukatar amincewa daga dukkan bangarori a yau," inda ta kara da cewa a farko ana sa ran amincewa da takardar yarjejeniya (MoU) da za a kammala ta hanyar intanet ta Pakistan, wadda ita ce kadai hanyar sadarwa a tattaunawar.

Yaki.
Yadda ake musayar wuta a yakin Iran, Amurka da Isra'ila Hoto: Anadolu
Source: Twitter

Shawarwarin da Pakistan ta kawo

A karkashin shawarar Pakistan, za a tsagaita wuta nan take kuma za a sake bude mashigar ruwa ta Hormuz, sannan za a bayar da kwanaki 15 zuwa 20 don kammala yarjejeniyar sulhu mai fadi.

Yarjejeniyar, wadda aka yi wa lakabi da "Islamabad Accord", za ta hada da tsarin kula da mashigar ruwan, tare da gudanar da tattaunawar karshe ido-da-ido a babban birnin Pakistan.

Majiyar ta ce ana sa ran yarjejeniyar karshe za ta hada da alkawarin Iran na kin kera makaman nukiliya, a madadin dage takunkumai da kuma sakin kudadenta da aka rike.

An kashe Shugaban leken asirin Iran

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Isra'ila babbar llla a mashigar Hormuz bayan babbake jirgin ruwanta

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaron Isra'ila sun tabbatar da cewa sun kashe Majid Khademi, Shugaban hukumar leken asiri na rundunar IRGC ta kasar Iran.

Majid Khademi ya mutu ne a wani harin da IRGC ta bayyana a matsayin "ta'addancin Amurka da Isra'ila," wanda aka kai ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026.

Kafin nada shi wannan matsayin, Khademi ya kasance shugaban wani sashe na hukumar leken asiri ta IRGC, wanda ke da alhakin sa ido kan harkokin cikin gida da dakile leken asirin kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262