Kasar Musulunci Ta Yi Rashi: Isra'ila Ta Kashe Shugaban Hukumar Leken Asirin Iran
- Jami'an tsaron Isra'ila sun tabbatar da cewa sun kashe Majid Khademi, Shugaban hukumar leken asiri na rundunar IRGC a wani harin sama
- Khademi shi ne shugaba na biyu da aka kashe a wannan matsayin cikin kasa da shekara daya, bayan kisan tsohon shugaba Mohammad Kazemi
- Ministan Isra'ila, Israel Katz, ya bayyana cewa za su ci gaba da farautar shugabannin Iran daya bayan daya domin rusa gwamnatin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran – Rundunar dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da mutuwar Shugaban hukumar leken asirinta, Majid Khademi.
Majid Khademi ya mutu ne a wani harin da IRGC ta bayyana a matsayin "ta'addancin Amurka da Isra'ila," wanda aka kai yau Litinin, 6 ga Afrilu, 2026.

Source: Twitter
Isra'ila ta kashe shugaban leken asirin Iran
Khademi ya zama babban jami'in IRGC na baya-bayan nan da ya hare-haren sama na hadin gwiwar Amurka da Isra'ila ya hallaka a Iran, in ji rahoton Reuters.

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
Ya karbi ragamar shugabancin hukumar ne a shekarar 2025, bayan da aka kashe magabacinsa, Mohammad Kazemi, a wani harin makamancin wannan a lokacin yakin kwanaki 12 na bara.
Kafin nada shi wannan matsayin, Khademi ya kasance shugaban wani sashe na hukumar leken asiri ta IRGC, wanda ke da alhakin sa ido kan harkokin cikin gida da dakile leken asirin kasashen waje.
Ya kuma rike manyan mukamai a ma'aikatar tsaron Iran, inda ake kallon sa a matsayin daya daga cikin mutane mafi iko a fannin tsaron kasar yau.
Isra'ila ta lashi takobi kan kasar Iran
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya tabbatar da cewa dakarunsu ne suka dauki ran Khademi, kamar yadda rahoton DW ya nuna.
Katz ya bayyana cewa:
"Rundunar kare juyin juya halin Musulunci na harbin iska ne kawai, farar hula suke kashewa, mu kuma muna kakkabe shugabannin 'yan ta'addan ne."
Ya kara da cewa shugabannin Iran za su ci gaba da zama cikin fargaba domin Isra'ila za ta farauto su daya bayan daya.
Martanin Iran da rikice-rikicen da take ciki
A daya bangaren kuma, makamai masu linzamin Iran sun kashe mutane biyu a birnin Haifa na Isra'ila a daren jiya Lahadi, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Source: Getty Images
Masana na ganin cewa kisan manyan jami'an Iran irin su Ali Larijani da Mohammad Pakpour babban koma-baya ne, kodayake tsarin sojan Iran na ba su damar ci gaba da kai hare-hare ko da shugabanninsu sun mutu.
Yayin da ake ci gaba da wannan yakin, hukumomin kare hakkin dan adam na duniya (HRANA) sun bayyana cewa akalla mutane 7,000 ne jami'an tsaron Iran suka kashe a lokacin murkushe zanga-zangar watan Janairu.
Yawan adadin da suka mutu ya sanya kasashen duniya ke kara matsin lamba kan gwamnatin Tehran, bisa zargin ta da tauye 'yancin d'an Adam.
Amurka, Isra'ila sun yi barna a Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, an shiga firgici a Iran bayan da Amurka da na Isra’ila suka kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan manyan biranen kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar tashin bama-bamai da kukan jiragen yaki na sa'o'i da dama a sararin samaniyar birnin Tehran yau.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 13 ne suka riga mu gidan gaskiya a wani harin da aka kai kusa da Eslamshar, dake kudu maso yammacin Tehran.
Asali: Legit.ng
