'Dan Majalisar Amurka Ya Hango Haɗarin Cigaba da Yaƙi da Iran

'Dan Majalisar Amurka Ya Hango Haɗarin Cigaba da Yaƙi da Iran

  • Wani ɗan majalisar wakilan Amurka, Jim McGovern na jam’iyyar Democrat ya yi gargaɗi cewa matakan soja a Iran na sa Amurkawa cikin haɗari
  • Jim McGovern ya soki kalaman Donald Trump na baya-bayan nan, yana mai cewa babu hankali a cikin bayanan Shugaban
  • Kalaman sun zo ne yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan yaƙin Amurka da Iran, musamman game da mashigar Hormuz

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Wani ɗan majalisar wakilan Amurka na jam’iyyar Democrat, Jim McGovern ya bayyana damuwa kan yadda gwamnatin Donald Trump ke tafiyar da harkokin soja a Iran.

Ɗan majalisar ya bayyana damuwa a kan halin da ake ciki, inda ya ce hakan na iya jefa rayuwar Amurkawa cikin haɗari maimakon kare su daga duk wata barazana.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya shiga yarjejeniya da kamfanin kamun kafa a Amurka a kan N1.9bn

Dan majalisar Amurka ya damu game da yaƙi da Iran
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Al-Jazeera ta wallafa cewa Jim McGovern ya ce irin wannan mataki na ƙara dagula rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, tare da janyo barazanar ramuwar gayya daga Iran ko ƙawayenta.

Da yake maidawa Trump martani a shafinsa na Facebook, McGovern ya yi tir da Shugaban na Amurka.

Ɗan majalisa ya damu kan yaƙin Amurka

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan siyasa a Amurka na ganin cewa tsauraran matakan soja da kalaman barazanar Trump na iya janyo ƙarin rikici da tashin hankali a duniya.

McGovern ya jaddada cewa duk wata manufa ta tsaro dole ne ta kasance mai rage haɗari ga ‘yan ƙasa, ba wai ƙara shi ba.

McGovern ya ce akwai matsala a tattare da Trump
Shugaban Amurka Donald Trump da ke yaƙi da Iran Hoto: Andrew Harnik/Getty Images
Source: Twitter

Baya ga batun soja, ɗan majalisar ya kuma caccaki kalaman Donald Trump na baya-bayan nan, waɗanda suka ƙunshi kalamai masu zafi da zagi kan Iran.

Ya bayyana irin waɗannan kalamai a matsayin na rashin hankali yana mai cewa ba su dace da shugabanci ba.

Kara karanta wannan

Iran ta nuna wa Trump yatsa, ta lalata hatsabiban jirage da Amurka ke ji da su

Shugaban Amurka na neman agaji – McGovern

A cewarsa, irin wannan kalami na Trump na iya tayar da hankali, ya kuma janyo matsaloli ga sojojin Amurka da ke wajen ƙasar, musamman idan suka faɗa hannun abokan gaba.

Ya bayyana cewa alamu sun bayyana ƙarara da ke nuna cewa Shugaban Amurka na buƙatar agaji idan aka duba kalamansa.

A baya-bayan nan, Trump ya yi barazana cewa zai saukarwa Iran ruwan hare-hare matuƙar ba ta bi umarninsa na buɗe mashigar Hormuz ba.

Amma ɗan majalisar McGovern ya bayyana cewa:

“Wannan hauka ne. Ana sanya Amurkawa a cikin haɗari."

Gargaɗin Amurka ga ƙasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald J Trump ya bai wa Iran wa’adin awa 48 ta bude hanyar wucewar jiragen ruwa ta mashigar hanyar ruwa Hormuz.

Shugaba Donald Trump ya yi gargadin cewa lokaci na kurewa Iran daga wa'adin da aka ba ta na bude mashigar Hormuz a cikin gaggawa ko ta gamu da tashin hankali.

Kalaman sun kara tayar da hankali kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya musamman bayan hare-hare kan wuraren makaman Iran da Isra'ila da Amurka ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng