Netanyahu Ya Yi Magana da Kasar Iran Ta Farmaki Muhimmin Wuri a Isra’ila
- Kasar Iran ta ce ta kai hari kan masana’antun sinadarai da kusa da Dimona a Isra’ila da ya jawo mata babbar asara
- Ta kuma kai hare-hare da jiragen drone kan sansanonin sojin Amurka a Kuwait wanda ya tsananta yakin da ake yi
- Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya tabbatar da hare-haren Isra’ila kan masana’antun Iran
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Tehran, Iran - Sojojin Iran sun bayyana cewa sun kai hari kan masana’antun petrochemical da ke kusa da Dimona a kudancin Isra’ila.
An ce Dimona na dauke da babban cibiyar nukiliyar Isra’ila, wanda ya kara nuna muhimmancin wurin da aka kai harin wanda ya jawo mata asara.

Source: Facebook
Sanarwar ta kuma ce sojojin Iran sun kai hare-hare da jiragen mara matuki kan wuraren sojin Amurka da ke tsibirin Bubiyan a kasar Kuwait, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Iran ta yi wa Isra'ila babbar llla a mashigar Hormuz bayan babbake jirgin ruwanta
Yadda yaki ta barke a Gabas ta Tsakiya
Hakan ya biyo bayan ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.
An fara kai hari ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki a birnin Tehran wanda ya yi sanadiyar mutuwar Ayatollah Ali Khamenei.
Baya ga rasa ran Khamenei, an rasa rayukan manyan jami'an tsaron Iran wanda daga bisani suka dauki matakin kai farmakin ramuwar gayya kan Amurka da Isra'ila.
Kasashen duniya da dama sun sha kiran da a tsagaita wuta a yakin da suke ganin yana shafar tattalin arzikin duniya bayan rufe mashigar Hormuz.
Abin da Netanyahu ya ce kan harin
A daya bangaren, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya tabbatar da cewa sojojin kasar sun kai hare-hare kan masana’antun petrochemical na Iran.
Ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da aka wallafa inda ya yi karin bayani kan matakan da Isra’ila ke dauka, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana
Netanyahu ya ce bayan sun lalata kashi 70% na karfin Iran na samar da karafa, sun ci gaba da kai hare-hare kan masana’antun petrochemical.
Ya kara da cewa wadannan bangarori biyu ne ke samar da kudaden da Iran ke amfani da su wajen gudanar da hare-haren da ya kira na ta’addanci.
Firaministan ya zargi Iran da amfani da wadannan kudade wajen daukar matakan yaki ba kawai kan Isra’ila ba, har ma da sauran kasashen duniya.
Iran ta kai hari wani kamfani a Isra'ila
A baya, mun ba ku labarin cewa wani Kamfani a Isra'ila ya tabbatar da cewa an kai hari masana’antarsa a kudancin kasar da makami daga Iran.
Gobara ta tashi a yankin masana’antu na Ne’ot Hovav bayan harin, inda jami’an kashe gobara 34 suka yi kokarin shawo kan lamarin.
Hukumomi sun ce an shawo kan gobarar, duk da lalacewar gini, yayin da aka gargadi jama’a su guji yankin saboda sinadarai masu hadari.
Asali: Legit.ng