Bayan Barazanar Trump, Iran Ta Kafa Sharadi 1 na Bude Mashigar Hormuz

Bayan Barazanar Trump, Iran Ta Kafa Sharadi 1 na Bude Mashigar Hormuz

  • Kasar Iran ta kafa sharadin bude mashigar Hormuz bayan barazana da Shugaba Donald Trump ya yi mata a kwanakin nan
  • Iran ta ce ba za ta bude mashigin Hormuz ba sai an biya diyya saboda barnar yaki da aka yi mata a wannan rikici
  • Wani jami’i ya ce za a kafa sabon tsarin doka inda za a rika karbar kudin wucewa kafin a sake bude mashigin ruwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta yi karin haske kan kiraye-kirayen da ake yi da ya bude mashigar Hormuz a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta bayyana cewa ba za ta sake bude mashigin ruwa na Hormuz ba sai an biya ta diyya kan barnar da aka yi mata sakamakon yakin da ke gudana.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana

Iran ta yi magana kan bude mashigar Hormuz
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Iran Military Media.
Source: Facebook

Seyyed Mehdi Tabatabaei, mataimaki na harkokin sadarwa a ofishin shugaban kasar Iran, ya ce za a biya kudin ne ta wani sabon tsarin doka, cewar Al Jazeera.

Yadda yaki ta barke a Gabas ta Tsakiya

Hakan ya biyo bayan ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

An fara kai hari ne a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 a Tehran wanda ya yi sanadiyar mutuwar Ayatollah Ali Khamenei.

Sharadin Iran kan bude mashigar Hormuz

Seyyed ya kara da cewa wannan tsarin zai dogara ne da kudin wucewa, inda jiragen ruwa za su rika biya kafin su samu damar wucewa.

Jami’in ya bayyana hakan ne ta wani sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta, yana mai jaddada cewa Iran ba za ta sassauta matsayinta ba.

Ya ce dole ne a cimma yarjejeniya kan diyya kafin a bude wannan muhimmiyar mashigar ruwa da ake jigilar mai a duniya.

Kara karanta wannan

Barazanar da Trump ya sake yi wa kasar Iran, ya fadi barnar da ya yi mata a yaki

A wani bangare kuma, Tabatabaei ya soki tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan barazanar da ya yi wa Iran.

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Barazanar da Donald Trump ya yi ga Iran

Trump ya yi barazanar kai hari kan cibiyoyin fararen hula na Iran bayan rufe mashigin Hormuz da aka yi, kamar yadda Daily Mirror ta ruwaito.

Sai dai jami’in na Iran ya bayyana kalaman Trump a matsayin marasa tushe da rashin kamun kai, yana mai cewa sun fito ne daga takaici da fushi.

Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai a duniya, kuma rufewarta na iya janyo matsala ga tattalin arzikin duniya.

Masana sun ce duk wani jinkiri wajen bude mashigin na iya kara dagula al’amuran siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mashigar Hormuz: Trump ya yi barazana ga Iran

Mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka, Donald J Trump ya bai wa Iran wa’adin awa 48 ta bude hanyar wucewar jiragen ruwa ta Hormuz.

Donald Trump ya yi gargadin cewa lokaci na kurewa Iran daga wa'adin da aka ba ta na bude mashƙƙuigar Hormuz a cikin gaggawa.

Kalaman sun kara tayar da hankali kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya musamman bayan hare-hare kan wuraren makaman Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com