Iran Ta Fadi 'Bazata' da Za Ta Yi wa Amurka a Yaƙi da Isra'ila bayan Mata Barazana

Iran Ta Fadi 'Bazata' da Za Ta Yi wa Amurka a Yaƙi da Isra'ila bayan Mata Barazana

  • Kasar Iran ta yi watsi da barazanar Donald Trump bayan ya ba ta wa'adin awa 48 kan tattaunawa da yake neman a yi
  • Iran ta kira hakan da rashin daidaito, tare da gargadin kai farmaki mai tsanani idan Trump ya aiwatar da abin da ya fada
  • Janar Ali Abdollahi ya ce Iran za ta kai farmaki mai muni kan Amurka da Isra’ila idan aka lalata kayayyakin more rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta yi fatali da barazanar shugaban Amurka, Donald Trump na lalata muhimman kayayyakin kasar.

Donald Trump ya yi wannan barazane ne ga Iran idan ba ta cimma yarjejeniya cikin awanni 48 ba.

Iran ta gargadi Amurka kan barazanar da ta yi mata
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Rahoton Al Jazeera ya ce Iran ta bayyana wannan gargadi a matsayin rashin daidaito da firgici, tana mai cewa matakin yana nuna rauni da gazawar dabarun Amurka a yakin da ake ci gaba.

Kara karanta wannan

Iran ta lissafo wuraren da za ta kai wa hari idan Amurka ba ta shiga taitayinta ba

Jami'in Iran ya gargadi Shugaba Donald Trump

Janar Ali Abdollahi Aliabadi daga hedikwatar “Khatam al-Anbiya” ya gargadi cewa duk wani hari daga Amurka ko Isra’ila zai fuskanci ramuwar gayya mai tsanani.

Ya ce sojojin Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare martabar kasa, suna masu cewa za su mayar da martani cikin gaggawa.

Ya kara da cewa idan har Amurka ta kai farmaki kan Iran to kasar za ta ba ta mamaki game da tanadin da ta yi na musamman.

Wani jami’in tsaro na Iran ya ce kasar na tafiya bisa tsari a yakin, tare da shirin bayar da wani babban mamaki ga Amurka da Isra’ila.

Ya kara da cewa dabarun Amurka sun gaza, yana mai cewa Iran ta kware wajen yaki irin na dabarun dabara domin gajiyar da abokan gaba.

Barazanar Trump ta fusata Iran a yakin da ake yi
Jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Wa'adin da Trump ya ba kasar Iran

A baya, Trump ya ba Iran wa’adin kwanaki 10 kafin ta bude mashigar Hormuz ko ta fuskanci mummunan hari daga Amurka.

Kara karanta wannan

Barazanar da Trump ya sake yi wa kasar Iran, ya fadi barnar da ya yi mata a yaki

Wannan mashiga tana da matukar muhimmanci domin kusan kashi 20 cikin dari na man fetur na duniya na ratsa ta zuwa kasuwanni daban-daban.

Rikicin ya fara ne bayan hare-haren Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, inda aka kai farmaki kan wasu wurare a cikin Iran, cewar NDTV World.

Tun daga lokacin, hare-hare da martani sun yi sanadin mutuwar dubban mutane a Iran da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun ce an harbo jiragen yaki na Amurka, yayin da aka ceci wani matukin jirgi daya, dayan kuma har yanzu ba a gano shi ba.

Haka kuma, an kai hari kusa da tashar nukiliya ta Bushehr, lamarin da ya sa aka kwashe ma’aikata saboda fargabar yaduwar radiation a yankin.

Trump ya magantu kan karkare yakin Iran

A wani labarin, an ji cewa shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na iya lalata tashar wutar lantarkin Iran cikin sa'a guda amma ta zabi ta kyale su.

Shugaban ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun ruguza kusan daukacin makaman da sojojin Iran suke takama da su wajen kai hari.

Trump ya jaddada cewa Amurka ta ceci kasar Isra'ila da ma daukacin yankin Gabas ta Tsakiya daga mamayar kasar Iran a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.