Bana ka Taba: Faransa Ta Tura Sojoji da Tankokin Yaki domin a Yaki Isra'ila

Bana ka Taba: Faransa Ta Tura Sojoji da Tankokin Yaki domin a Yaki Isra'ila

  • Gwamnatin Faransa ta cika gagarumin alkawarin da ta yi wa Lebanon yayin da Isra'ila ke cigaba da kashe fararen hula a fadin kasar
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Emmanuel Macron ta sanar da tura tankokin yaki sama da 30 dauke da sojoji domin yakar Isra'ila
  • Sojojin Isra'ila karkashin Benjamin Netanyahu sun kai hare-hare kasar Lebanon tun bayan fara yakin Iran, lamarin da ya ja hankalin duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lebanon - Faransa ta mika motocin yaki guda 39 ga rundunar sojin Lebanon domin cika alƙawarin da jami’an kasar suka yi a baya, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta sanar a ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, lamarin da ya sanya dakarun Tel Aviv kai hare-hare Lebanon.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuta, Trump ya nemi a tsagaita wuta a yakin da ake da Iran

Tankokin yakin da Faransa ta ba Lebanon
Yadda Faransa ta ba Lebanon motocin yaki saboda hare-haren Isra'ila. Hoto: @RufoAlice
Source: Twitter

Dalilin tura sojojin Faransa Lebanon

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa mataimakiyar ministan tsaron Faransa, Alice Rufo, ta ce wannan mataki na nufin kare ikon ƙasar Lebanon.

Faransa ta kara da cewa sojojin za su kare rayukan fararen hula ba tare da la’akari da addininsu ba, da kuma tabbatar da dorewar cibiyoyin gwamnatin kasar.

Alice Rufo ta bayyana hakan ne yayin bikin miƙa motocin a tashar jiragen ruwa ta Beirut a ranar Talatar da ta wuce kamar yadda ta wallafa a X.

Wuraren da sojojin za su yi aiki

Motocin, da ake kira VABs, an ƙera su ne domin sauƙaƙa motsin sojoji da kuma ba su damar gudanar da ayyuka a wuraren da ke da haɗari sosai.

Kowace mota na iya ɗaukar kusan sojoji 10 cikakku da kayan aiki, kuma an yi su da ƙarfe mai ƙarfi domin kare sojojin daga harbin bindiga da fashewar ƙananan bama-bamai.

Kara karanta wannan

Abubuwan sun cabe, an fara lalubo hanyoyin lallaba kasar Iran ta yi sulhu da Amurka

A ƙarshen watan Maris, shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da tallafawa rundunar sojin Lebanon, ciki har da isar da irin waɗannan motocin, yana mai jaddada muhimmancin kare cikakken ikon ƙasar.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron
Emmanuel Macron ba buga waya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A halin yanzu, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren sama a Lebanon tare da ƙaddamar da farmakin ƙasa a Kudancin ƙasar, bayan wani hari da Hezbollah ta kai a kan iyaka a ranar 2 ga Maris, 2026.

Arab News ta wallafa cewa sabon tashin hankali ya biyo bayan farmakin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila da aka fara a ranar 28 ga Fabrairun 2026 a kan Iran, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 1,340.

Trump ya nemi a daina yakin Iran

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta bukaci shugabannin Iran su dakatar da yakin da ake na wasu sa'o'i.

Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da wata guda ana gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da matsin tattalin arziki.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Iran ta mayar da martani da harba bama-bamai maimakon yarda da tayin tsagaita wuta da Amurka ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng