Amurka Ta Ji Wuta, Trump Ya Nemi a Tsagaita Wuta a Yakin da ake da Iran
- Rahotanni sun nuna kasar Amurka karkashin shugaba Donald Trump ta nemi a tsagaita wuta a yakin da aka fara a karshen watan Fabrairun 2026
- Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana gwabza fadan da ya jawo mutuwar mutane da dama da lalata kadarorin biliyoyin daloli a duniya
- Shugaba Donald Trump ya yi bayani game da harbo jirgin Amurka da dakarun Iran suka yi da makomar sulhun da ya ce an fara maganar shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kasar Amurka ta gabatar da wani kudiri ga Iran domin a tsayar da yakin da Donald Trump da Benjamin Netanyahu suka kaddamar a Iran.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin Iran sun yi wa Amurka martani maras dadi, inda sojojin kasar suka cigaba da harba makamai Isra'ila.

Source: Facebook
Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa hare-haren da Iran ta kai kasashen Gabas ta Tsakiya sun shafi sansanin sojojin Amurka bayan maganar tsagaita wutar.
Amurka ta nemi Iran ta tsagaita wuta
Amurka ta gabatar da shawarar tsagaita wuta na sa'o'i 48 ga Iran a ranar 2 ga Afrilun 2026, kamar yadda kamfanonin yada labarai da dama suka ruwaito a ranar Juma’a.
Majiyar ta ce:
“Amurka ta gabatar da wannan shawara ta tsagaita wuta ta sa'o'i 48 ta hanyar wata ƙasa a ranar 2 ga Afrilu,”
Majiyar ta ƙara da cewa an gabatar da shawarar ne bayan ƙara tsanantar rikici da ƙalubalen da sojojin Amurka ke fuskanta a yankin.
Martanin Iran ga kasar Amurka
A cewar wani rahoto, Iran ba ta mayar da martani a rubuce ba, sai dai ta mayar da martani “a filin daga” ta hanyar ci gaba da kai hare-hare masu tsanani.
Majiyar ta kuma ce ƙoƙarin Amurka na dakatar da faɗan ya ƙaru, musamman bayan wani rahoton hari da aka kai kan wani rumbun ajiyar kayan sojin Amurka a tsibirin Bubiyan da ke Kuwait.
Maganar Trump kan sulhu da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce lalacewar wani jirgin yaƙin Amurka ba zai shafi tattaunawar diflomasiyya da Iran ba, kamar yadda ND TV ta ruwaito.
Ya ƙaryata cewa lamarin zai kawo cikas ga tattaunawar, yana mai cewa:
“A’a, ko kaɗan. Wannan yaƙi ne. Muna cikin yaƙi.”
Rahoto ya nuna cewa wannan shi ne karo na farko da ya yi magana a bainar jama’a kan asarar jirgin yaƙin Amurka a lokacin yakin.

Source: Facebook
Trump ya ƙi yin cikakken bayani kan ceto matukin jirgin, yana mai cewa lamarin na da matuƙar muhimmanci, sannan ya nuna rashin jin daɗi kan yadda kafafen yaɗa labarai ke fitar da rahoto kan lamarin.
Trump ya zargi mataimakinsa
A wani labarin, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya dage da magana kan sulhu da Iran yayin yakin da ake cigaba da gwabzawa.
Trump na maganar sulhun ne duk da cewa shugabannin Iran na maimaita cewa ba su shiga wata tattaunawa da Amurka kai tsaye ba.
A wani taro a fadar White House, Trump ya ce idan aka gaza cimma yarjejeniya da Iran, mataimakinsa, JD Vance ne abin zargi ba shi ba.
Asali: Legit.ng

