Matukan Jirgin Amurka da Aka Kakkabo na tsaka Mai Wuya, Iran Ta Sa Kyauta Mai Tsoka

Matukan Jirgin Amurka da Aka Kakkabo na tsaka Mai Wuya, Iran Ta Sa Kyauta Mai Tsoka

  • Hukumomin Iran sun sanya kyauta mai tsoka ga duk wanda ya bada bayanai ko ya kama matukar jirgin Amurks da aka kakkbo
  • Rahoto ya nuna cewa Iran ta harbo jirgin ya rikito kasa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta a Gabas ta Tsakiya
  • Amurka ta yi ikirarin cewa ta ceto daga daga cikin matukan jirgin guda biyu yayin da Iran ta fara farautar dayan ko kuma duka biyun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - A yau Juma'a, 3 ga watan Afrilu, 2026 aka samu rahoton cewa dakarun sojojin Iran sun kakkabo jirgin yaki na kasar Amurka.

Bayanai sun nuna cewa matukan jirgin sun bata bayan hatsarin, amma daga bisani Amurka ta yi ikirarin cewa ta ceto daya daga ciki.

Jirgin Amurka.
Jirgin yakin kasar Amurka yayin da ya fara tashi daga filin jirgin sama Hoto: U. S Navy
Source: Twitter

Iran ta fara farautar makutan jirgin Amurka

Kara karanta wannan

Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka, an sanya ladar kudi ga wanda ya kamo matuƙan

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hukumomin kasar Iran sun kaddamar da gagarumin bincike da farautar matukan jirgin yakin Amurka wadanda dakarun kare juyin juya hali suka kakkabo.

Rahotanni sun nuna cewa an tura dakarun soji tare da yin alkawarin ba da kyauta mai tsoka ga duk wanda ya kamo su.

Kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito cewa dakarun musamman na Amurka sun yi nasarar ceto daya daga cikin ma'aikatan jirgin su biyu.

A daya bangaren kuma, gidan talabijin na lardin Kohgiluyeh da ke Kudancin kasar Iran, ya nuna hotunan abin da ya ce baraguzan jirgin yakin ne da aka kakkabo.

Yadda aka fara yakin Iran da Amurka

Wannan yaki tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila ya barke ne a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, fiye da wata guda kenan da ya gabata.

Amurka da Isra'ila ne suka fara kai hare-hare kan kasar Iran wadanda suka yi sanadin mutuwar Jagoran kass, Ayatollah Ali Khamenei.

Wannan lamari ya sa Iran ta fara kai jerin hare-haren mayar da martani, kuma hakan ya jawo fadada rikicin zuwa sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Kasar Isra'ila ta aikata mummunan laifi, ta kai farmaki masallaci a ranar Juma'a

Sojojin Iran.
Sojojin Iran suna fareti a ranar bikin sojoji a birnin Tehran Hoto: ATTA KENARE
Source: Getty Images

Iran ta sanya kyauta mai tsoka

Rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM), ta yi jinkirin yin tsokaci kan batar matukan jirgin yayin da aka tuntube ta kamar yadda Al-Jazeera ta rahoto.

Wani dan jarida na gidan talabijin din Iran ya sanar da cewa:

"Ya ku mutane masu daraja na lardin Kohgiluyeh da Boyer-Ahmad, duk wanda ya kamo matukin jirgin makiya ko matukan jirgin su biyu da ransu ya mika su ga 'yan sanda ko sojojin Iran, zai samu kyauta mai tsoka da kuma garabasa."

Iran ta ci gaba luguden wuta a Isra'ila

A baya, kun ji cewa rundunar sojojin kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta farmaki biranen Tel-Aviv da Haifa na Isra'ila.

IRGC ta kai hare-haren ne a matsayin rukuni na 91 na jerin ayyukanta na Operation True Promise 4, inda ta farmaki tsakiyar biranen Tel Aviv da Haifa na Isra'ila.

Ta bayyana cewa hare-haren sun tilasta wa mazauna Isra'ila kusan miliyan 5 neman mafaka a cikin ramin buya na karkashin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262