Ana tsaka da Yak, An Bayyana Kasar da Ta Samu Nasara tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila
- Tsohon ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif ya bai wa Jamhuriyar Musulunci shawarwarin yadda za ta kawo karshen yaki da Amurka/Isra'ila
- Zarif ya bukaci Iran ta ayyana kanta a matsayin wacce ta samu nasara, sannan ta kafa sharuddan yayin tattaunawa da Amurka da Isra'ila
- Wannan na zuwa ne bayan shafe sama da wata guda ana musayar wuta, lamarin da ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin babban tashin hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Tsohon Ministan Harkokin Wajen Iran, Javad Zarif, ya ayyana kasarsa a matsayin wacce ta samu galaba a yakin da take da kasashen Amurka da Isra'ila.
Zarif ya bukaci kasar musulunci ta Iran da ta "ayyana nasara tare da kulla yarjejeniyar da za ta kawo karshen wannan rikici da kuma hana barkewar wani a nan gaba."

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a ciki wata kasidarsa da aka wallafa yau Juma'a, 3 ga watan Afrilun 2026, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Tsohon ministan ya tsara wani tsari tare da shawarwari da ya bayyana a matsayin taswirar yadda Iran za ta kawo karshen yaki da Amurka da Isra'ila a kan sharuddan da za su amfani Tehran.
Muhimman shawarwarin Javad Zarif ga Iran
1. Yarjejeniyar nukiliya da mashigar ruwa ta Hormuz: Ya ba da shawarar cewa Iran ta rage karfin shirin nukiliyarta sannan ta sake bude mashigar ruwa ta Hormuz, muddin za a dage dukkan takunkuman da aka sanya mata.
A cewar tsohon ministan, watakila kasar Amurka za ta amince da wadannan sharudda a yanzu koda kuwa ta ki hakan a baya.
2. Yarjejeniyar dakatar da kai hare-hare: A cewarsa, ya kamata Iran ta amince da kulla yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka wacce za ta tanadi kin kai wa juna hari a nan gaba.

Kara karanta wannan
Abubuwan sun cabe, an fara lalubo hanyoyin lallaba kasar Iran ta yi sulhu da Amurka
3. Kulla alakar tattalin arziki: Javad Zarif ya ba da shawarar bude kofofin kasuwanci da Amurka, wanda a cewarsa zai zama nasara ga al'ummar kasashen biyu.

Source: Getty Images
Amfanin kafa wadannan sharudda ga Iran
A cewar Zarif, wadannan matakai za su ba jami'an Iran damar rage mayar da hankali kan tsaron kasa daga makiya, su koma mayar da hankali wajen inganta rayuwar al'ummar kasarsu a gida.
A cewarsa, matukar Iran ta samu damar kulla wadannan yarjejeniyoyi, hakan zai kara tabbatar da nasarar da ta samu a yakin da aka shafe fiye da wata guda ana gwabzawa, cewar rahoton NBC News.
Iran ta sake harba makamai akalla 300
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar IRGC ta Iran ta sanar da harba makamai masu linzami da suka haura 100 tare da rokoki 300 kan sansanonin sojin Amurka da Isra'ila.
IRGC ta tabbatar da cewa hare-haren sun daki muhimman wurare, ciki har da wani katafaren ginin sojin Amurka dake ƙasar Bahrain.
Rundunar sojin ta Iran ta kuma yi gargaɗi cewa waɗannan ayyukan soji za su ci gaba da gudana cikin "cikakken ƙarfi da izza" muddin ba a daina kai wa shugabannin Iran hari ba.
Asali: Legit.ng
