Iran Ta Harbo Hatsabibin Jirgin Amurka daga Sama, Ya Fado Kasa Ya Wargaje

Iran Ta Harbo Hatsabibin Jirgin Amurka daga Sama, Ya Fado Kasa Ya Wargaje

  • Rahotanni da suka Ira fito daga Tehran sun nuna cewa dakarun Iran sun yi nasarar harbo wani jirgin sojojin Amurka samfurin F-35 daga sama
  • Hakan na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kan cewa zai cigaba da lalata muhimman wurare a Iran
  • A daya bangaren, an samu rahotanni da suka nuna cewa an ka hari da jirgi maras matuki wata matatar mai da ke yankin Al Ahmad na Kuwait

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran - Iran ta sanar da kaddamar da sababbin hare-hare kan wasu wurare, ciki har da masana’antun ƙarfe mallakin Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma wata masana’antar makamai a Isra’ila.

Bugu da kari, sojojin Iran sun sanar da cewa sun kai farmaki kan jirgin Amurka da ya keta sararin samaniyarsu da nufin kai hari.

Kara karanta wannan

Yaki ya canza salo, kasar Iran ta bullo da dabarun ruguza shirin sojojin Amurka

Wani jirgin Amurka na yawo a sararin samaniya.
Yadda jirgin Amurka ke tafiya a sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Royal English News ya nuna cewa dakarun Iran sun ce da kyar wadanda suke cikin jirgin su rayu lura da halin da ya shiga bayan harbo shi.

Kasar Iran ta harbo jirgin Amurka

Dakarun IRGC na Iran sun yi iƙirarin cewa sun sake harbo wani jirgin yaƙi na Amurka samfurin F-35 a yayin da yake shawagi a tsakiyar kasar su.

Wani saƙo suka wallafa ya ce jirgin ya lalace gaba ɗaya, ya faɗo, kuma babu wani bayani kan matuƙin jirgin saboda irin ɓarnar da ta faru.

Wasu bayanai da suka fito daga dakarun sun nuna cewa da alama matuƙin jirgin bai samu damar yin tsalle ya fita daga cikinsa ba saboda fashewar da ta biyo bayan haɗarin.

Amurka ba ta ce komai ba

Sai dai rundunar sojin Amurka ta USCC ba ta yi martani kai tsaye ba, amma ta ƙaryata wani iƙirari na baya daga IRGC cewa sun harbo jirgin yaƙin Amurka.

Kara karanta wannan

Trump: Amurka ta tsara shiga Iran da dubban sojoji da kayan tono sinadarai

Rundunar USCC ce ke jan ragamar yakin da Amurka ta hada kai da Isra'ila ta kaddamar a Iran tun ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Sojojin Amurka tare da Donald Trump
Shugaba Donald Trump na yi wa sojojin Amurka bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An lalata matatar mai a Kuwait

Tashar Al-Jazeera ta wallafa cewa da safiyar yau Juma'a 4 ga watan Afrilu, 2026 an kai hari da jirgi maras matuƙi kan wata matatar mai da ke Al Ahmadi, wadda kamfanin Kuwait ke gudanarwa.

Rahoton ya ce harin ya janyo gobara a wasu sassan matatar, amma babu ma’aikacin da ya jikkata kuma an tura jami’an agaji da na kashe gobara zuwa wurin domin shawo kan lamarin.

A wani saƙo da aka fitar daga baya, an yi gargadin cewa ana ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa Kuwait.

Iran: Trump ya zargi mataimakinsa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake magana kan kokarin da ya ce suna yi wajen shawo kan Iran.

Ya sanar da cewa idan aka gagara samun yarjejeniya da Iran domin tsayar da yakin, ba wanda ya kamata a zarga sai mataimakinsa, JD Vance.

Sai dai Trump ya ba masu sauraron bayanin da ya yi mamaki da ya ce idan aka samu nasarar shawo kan Iran, dole shi za a jinjinawa.

Wanda ya tantance Nicolette Marais, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng