Amurka Ta Gamu Matsala, Iran Ta Farmaki Manyan Jiragen Yakin da Take Ji da Su
- Ana ci gaba da.musayar wuta a yakin da ake yi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran a yankim Gabas ta Tsakiya
- Rundunar sojojin Iran ta kaddamar da hare-hare ta hanyar amfani da jirage marasa matuka kan jiragen yakin Amurka
- An kaddamar da hare-haren ne kan sansanin sojojin Amurka da ke Jordan wanda ke dauke da kwararrun jiragen yaki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar sojojin ƙasar Iran ta tabbatar da ƙaddamar da harin jirage marasa matuƙa kan jiragen yaƙin Amurka.
Rundunar sojojin ta Iran ta kai harin ne kan jiragen yakin da ke jibge a wani sansanin sojojin Amurka a ƙasar Jordan.

Source: Twitter
Tashar Press tv ta kasar ta kawo rahoton cewa an kai harin ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026.
Iran ta farmakin sansanin sojin saman Amurka

Kara karanta wannan
Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila
A cikin sanarwa ta 52 a hukumance tun bayan fara fafatawar, rundunar sojojin ta sanar da cewa jiragenta marasa matuƙa sun farmaki sansanin sojojin sama na al-Azraq, wanda babban matattarar sojin Amurka ne a gabashin Jordan.
Wannan sansanin dai an san shi da ingantattun kayan aiki da kuma yawan jami'an sojoji, wanda hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin mafi muhimmancin wuraren soja na Amurka a Yammacin Asiya.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“A sa'o'in farko na ranar Alhamis, jajirtattun sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kai hari kan ƙwararrun jiragen yaƙi na sojojin ta'addanci na Amurka da ke jibge a sansanin al-Azraq a Jordan ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa."
Wane muhimmanci sansanin yake da shi?
Sanarwar ta jaddada mahimmancin sansanin na al-Azraq, wanda ke taka rawa wajen tsara hare-haren sama na Amurka, gami da amfani da manyan jiragen yaƙi da na’urori marasa matuƙa wajen kai hari kan Iran, tashar WANA ta kawo labarin.

Source: Getty Images
A cewar rundunar sojojin, an kai harin ne da nufin raunana ƙarfin abokin gaba na yin yaƙi ta sama.
A makon da ya gabata ma, rundunar sojojin Iran ta ƙaddamar da wani harin na daban a al-Azraq, inda ta farmaki rumbun adana kayan aiki, da wuraren kwanan sojojin Amurka da ke sansanin.

Kara karanta wannan
Iran ta samu tagomashi, sojojin wata kasa sun shirya kawo mata dauki kan yaki da Amurka
Iran ta shigar da korafi kan Jordan
A ranar 22 ga Maris, Iran ta shigar da ƙara a hukumance ga majalisar dinkin duniya da kuma kwamitin tsaro kan rawar da Jordan ke takawa wajen sauƙaƙa wa Amurka kai hare-hare kanta.
Jakadan Iran a majalisar dinkin duniya, Amir Saeed Iravani, ya yi kira ga Jordan da ta daina ba da kowane nau’in taimako ga waɗannan ayyuka nan take, sannan ta hana amfani da ƙasarta ko sararin samaniyarta wajen kai hari kan Iran.
Trump ya kori Antoni Janar
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kori Antoni Janar daga mukaminta.
Shugaba Donald Trump ya sanat da cewa Pam Bondi za ta bar mukaminta na Antoni Janar daga ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilun 2026.
Donald Trump ya kuma sanar da cewa mataimakin Antoni Janar, Todd Blanche, shi ne zai karbi ragamar ma'aikatar a matsayin mai rikon kwarya.
Asali: Legit.ng