Barazanar Tsaro: Dan Amurka da aka Ce an Kora daga Najeriya Ya Tabo Sheikh Gumi
- Dan kasar Amurka da ya ke yawo a kauyukan Arewacin Najeriya, Alex Barbir ya sanar da cewa yana hanyar komawa gida bayan zargin da aka yi masa
- Yayin da ake kokarin barin Najeriya, Alex ya yi martani ga malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi da hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad
- Sai dai bayan maganganun da ya yi, Bashir Ahmad ya yi ikirarin cewa jam'ian tsaro ne suka fatattake shi daga kasar nan bayan zarge-zargen dake kan shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hadimin tsohon shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya yi iƙirarin cewa an fatattaki dan Amurka da ke yawo a Najeriya yana kira a dauki makami, Alex Barbir.
Bashir Ahmad ya zargi Alex Barbir da ƙoƙarin haifar da rikicin addini a wasu al’ummomi a yankin Arewa ta Tsakiya bayan hango shi a wajen da aka kai hari a Filato.

Source: Twitter
Legit Hausa ta gano cewa Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis, 2 ga Maris, 2026.
Alex Barbir ya yi martani ga Ahmad Gumi
A yayin da yake barin Najeriya, Alex ya rubuta sako ga malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da Bashir Ahmad, inda ya alakanta su da 'yan ta'adda.
A sakon da ya wallafa a X, ya ce:
“Bashir da Gumi! Yanzu da na bar ƙasar ku, ina sa ran Najeriya za ta zauna lafiya! Babu kisa, ba satar mutane, ƙone-ƙone, bam-bamai, ko hare-hare...”
Martanin Bashir Ahmad ga Alex
A martanin da ya yi, Bashir Ahmad ya nuna cewa hukumomi ne suka bukaci Alex ya bar Najeriya cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce:
"Ba ka bar ƙasar nan da son ranka ba, ka bar ta ne saboda hukumomi sun umurce ka da ka fice nan take, wani abu da ka musanta jiya da dare domin girman kai.
"Alex, mun san ka zo Najeriya da wata manufa bayyananniya ta tayar da rikici ta hanyar jefa mu gaba da juna, amma kamar yadda ya faru da wasu kafin ka, wannan manufa ba za ta yi nasara ba. Najeriya ta fi ƙarfinka, har ma da waɗanda suka aiko ka."

Source: Facebook
Karin korafi kan Alex Barbir
Bayan Bashir Ahmad, wasu 'yan Najeriya da dama sun yi korafi game da yadda Alex ya isa wajen da aka kai hari kafin zuwan jami'an tsaro.
Ga abin da Misbahu El-Hamza ya wallafa a Facebook:
“Alex Barbir ya zo Jos, ya isa wajen da aka aikata laifi kafin ma ‘yan sanda da ke kusa da wurin, sannan ya hura wutar rikici a zukatan matasa har suka fara ɗaukar makamai suna fafatawa da juna."
An bukaci a kama Alex Barbir
A wani labarin, kun ji cewa 'yan Najeriya sun harzuka bayan wani bidiyo da dan Amurka, Alex Barbir ya yi a lokacin da aka kai hari Filato.
'Dan kasar Amurkan ya fito a wani bidiyo yana sukar gwamnatin Najeriya da shugaba Bola Tinubu da cewa sun yi sakaci da matsalar tsaro.
'Dan jarida, Yushau Shuaib na cikin 'yan Najeriya da suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai a kan Alex da abin da ya ke a kasar nan.
Asali: Legit.ng

