Iran Ta Nuna Tsaurin Ido, Ta Sake Kunyata Trump a Idon Duniya

Iran Ta Nuna Tsaurin Ido, Ta Sake Kunyata Trump a Idon Duniya

  • Shugaba kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa mahukunta a Iran sun tunutube shi domin a tsagaita wuta
  • Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fito ta yi martani kan ikirarin na Donald Trump kan yakin da ake ci gaba da gwabzawa
  • Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya kuma bayyana kuskuren da Amurka ta yi wajen fara yakin

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta yi martani kan ikirarin Donald Trump, dangane da yakin da ake yi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi watsi da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump na cewa Tehran ta nemi tsagaita wuta, inda ya bayyana hakan a matsayin "ƙarya mara tushe."

Iran ta karyata Donald Trump
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton martanin na kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran a ranar Laraba, 1 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Me Trump ya ce kan Iran

Kalaman na sa na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka ya yi ikirarin cewa Iran ta nemi a tsagaita wuta kan yakin da ake yi.

Trump ya bayyana cewa shugaban kasar Iran ya tuntube shi yana neman a tsagaita wuta a yakin wanda aka kwashe fiye da wata daya ana gwabzawa.

Wane martani Iran ta yi?

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ce Amurka ta shiga yaƙin ne sakamakon "kuskuren lissafi" na Isra'ila, jaridar The Express ta dauko rahoton.

Esmaeil Baghaei ya bayyana kuskuren lissafi da matsin lamba daga ɓangaren Isra'ila ne ya janyo Amurka cikin wannan rikici. Kakakin ya kuma soki Amurka kan yadda take amfani da diflomasiyya ta hanyar da ba ta dace ba.

“Babu wani a duniya da zai iya sake amincewa da diflomasiyyar Amurka. Suna amfani da diflomasiyya da tattaunawa ne kawai a matsayin matakin farko na ɗora buƙatunsu ko amfani da ƙarfin soja."

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Daga karshe an bayyana kasar da sabon jagoran addini na Iran yake

- Esmaeil Baghaei

Haka zalika, ya iƙirarin cewa sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, yana cikin ƙoshin lafiya, kuma bai bayyana a fili ba ne kawai saboda yaƙin da ake yi.

Iran ta karyata Trump kan tsagaita wuta
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Iran ba ta shirya tattaunawa da Amurka ba

Esmaeil Baghaei ya ƙara da cewa al'ummar Iran ba su shirya yin maganar tattaunawa ko diflomasiyya da Amurka ba, wadda ta yi amfani da tattaunawar baya a matsayin hanyar share fage wajen ɗora sharuɗɗanta da yin amfani da ƙarfi.

Ya bayyana cewa harin da aka kai wa makarantar 'yan mata ta Shajareh Tayyebeh da ke Minab, wanda ya kashe aƙalla mutane 170, misali ɗaya ne kawai na ayyukan rashin imani da Amurka ta tafka a cikin watan da ya gabata.

Iran ta harbo jirgin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi ikirarin harbo wani jirgin sama mara matuki na Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa an harbo jirghin ne mai suna “LUCAS” a birnin Khorramabad da ke lardin Lorestan.

Jirgin “LUCAS” na daga cikin jiragen yaki marasa matuki masu araha, wanda ake kira “kamikaze” ko kuma makamin da ke shawagi kafin kai hari, domin yana kai hari ne ta hanyar fashewa da zarar ya bugi abin da aka nufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng