Yaki Ya Rincabe: Iran Ta Harba Makamai 300 Lokaci 1 kan Sojojin Amurka da Isra'ila

Yaki Ya Rincabe: Iran Ta Harba Makamai 300 Lokaci 1 kan Sojojin Amurka da Isra'ila

  • Rundunar IRGC ta Iran ta sanar da harba makamai masu linzami da suka haura 100 tare da rokoki 300 kan sansanonin sojin Amurka da Isra'ila
  • Rahotanni sun nuna cewa an lalata jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a sansanin Al-Adiri dake kasar Kuwait yayin harin daren Laraba
  • Iran dai ta gargadi ma'aikatan Google, Microsoft dake Gabas ta Tsakiya da su yi ta kansu domin za ta kai hare hare kan kamfanonin Amurka 18

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da ƙaddamar da wani sabon mataki na yaƙi, inda ta yi ruwan wuta kan wurare daban-daban na sojin Amurka da Isra'ila a faɗin yankin Tekun Fasha.

A wannan gagarumin hari, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar dakarun "resistance fronts," an yi amfani da makamai masu linzami sama da 100, jirage marasa matuƙa, da kuma wasu rokoki 200.

Kara karanta wannan

Yaƙi ya ɗauki zafi: Iran ta lissafa manyan kamfanonin Amurka 18 da za ta farmaka

Iran ta harba makamai sama da 300 kan sansanonin sojojin Amurka da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.
Wasu makamai masu linzami da Iran ta harba kan birnin Tel Aviv na Isra'ila. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Image
Source: Getty Images

Iran ta farmaki sansanonin Amurka, Isra'ila

Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta ruwaito, IRGC ta tabbatar da cewa hare-haren sun daki muhimman wurare, ciki har da wani katafaren ginin sojin Amurka dake ƙasar Bahrain.

Haka zalika, makai sun fada kan sashen jirage masu saukar ungulu na dakarun Amurka dake sansanin al-Adiri a ƙasar Kuwait, inda Iran ta yi ikirarin lalata aƙalla jirgi guda ɗaya.

Rundunar ta IRGC ta yi gargaɗi cewa waɗannan ayyukan soji za su ci gaba da gudana cikin "cikakken ƙarfi da izza" muddin ba a daina kai wa shugabannin Iran hari ba.

Barazana ga kamfanonin Amurka

Sa'o'i kaɗan kafin wannan babban hari, rahoto daga Legit Hausa ya nuna cewa Iran ta riga ta fitar da jerin sunayen kamfanonin fasaha da na tsaro na Amurka guda 18 waɗanda ta ayyana a matsayin halattattun wuraren kai hari.

Iran ta ba ma'aikata da mazauna kusa da waɗannan kamfanoni shawara da su nisanci wuraren da aƙalla kilomita guda domin tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Iran ta yi luguden wuta kan Amurka da Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare

Jerin wasu daga cikin kamfanonin da ake bibiya sun haɗa da: Google, Meta (Facebook), Apple, Microsoft, Intel, Nvidia, Tesla, Boeing, Cisco, HP, Dell, IBM da Oracle.

Makamai sama da 300 da Iran ta harba sun daki sansanonin Amurka da Isra'ila.
An samu tashin hayaki bayan saukar wani makami da Iran ta harba a tsakiyar Isra'ila. Hoto: Alexi Rosenfeld/Getty Images
Source: Getty Images

Lalata ababen more rayuwa a Iran

A ɗaya ɓangaren kuma, ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ta bayar da rahoton cewa hare-haren sama da aka kai cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun lalata sama da cibiyoyin farar hula 92,000, ciki har da makarantu da asibitoci.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa yaƙin ya shiga wani sabon babi na lalata muhimman gine-ginen tattalin arziki, in ji rahoton The Times of India.

An kai hari kan kamfanonin haɗa magunguna a Tehran da kuma masana'antun ƙarfe dake Isfahan da Khuzestan.

IRGC: Iran ta yi wa Isra'ila barna

A wani labari, mun ruwaito cewa, makamai masu linzami na Iran sun daki wani babban gini a Bnei Brak inda aka kwashe yara da mata zuwa asibiti bayan sun ji rauni.

Hukumar MDA ta tabbatar da jikkatar mutane tara a sassan Tel Aviv da Petah Tikva sakamakon barbashin makaman da suka tarwatse.

Dakarun sojin Isra'ila sun gano ƙarin makamai daga Iran dake tunkarar sassan kudancin ƙasar bayan harin da aka kai tsakiyar ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com