Isra'ila Ta Bar Boye Boye, Ta Bayyana Adadin Waɗanda Suka Jikkata a Yaki da Iran
- Kasar Isra'ila ta fitar da adadin wadanda suka jikkata yayin yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo asarar rayuka
- Ma'aikatar lafiya ta ce dubban mutane sun jikkata yayin da rikicin yaki ke ci gaba tun daga karshen watan Fabrairun 2026
- Isra’ila ta ce mutane da dama na kwance a asibiti, ciki har da 18 cikin mawuyacin hali, yayin da sojoji 10 suka mutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Ma'aikatar lafiya a Isra'ila ta fitar da gamsassun bayanai game da wadanda suka jikkata a yaki.
Ma'aikatar ta ce adadin wadanda suka jikkata a Isra’ila ya kai 6,131 yayin da ake ci gaba da yaki da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Rahoton Al Jazeera ya ce rikicin hadin gwiwar hare-haren soji tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran a yankin ne ya jawo haka.
Asarar da aka yi a yakin Iran/Isra'ila
Rahotanni sun ce wannan sabon rikici ya fara ne a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, lokacin da shugaban Amurka Donald Trump tare da shugabannin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran.
An ce hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei tare da wasu manyan jami’an gwamnati, abin da ya kara tayar da hankula a yankin.
A martaninta, Iran ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan Isra’ila da kuma sansanonin sojin Amurka da kawayenta da ke kasashe irin su Saudiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sauran wuraren da aka kai hari sun hada da Oman, Bahrain, Iraki da Cyprus, lamarin da ya janyo hankalin duniya kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya da hanyoyin makamashi na duniya.

Source: Facebook
Illar da Iran ta yi wa Isra'ila a yaki
Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta fitar da sababbin alkaluma ta shafukan sada zumunta, cewar Anadolu Ajansi.
Tana mai bayyana halin tsaro yana da matukar sarkakiya a yankin Gabas ta Tsakiya da ake yaki wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
A cewar ma’aikatar, mutane 118 na ci gaba da karbar magani a asibitoci daban-daban a Isra’ila, inda aka ce mutane 18 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
Haka kuma, an bayyana cewa adadin sojojin rundunar tsaron Isra’ila da suka mutu tun daga ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 ya kai 10, wanda ke nuna tsananin rikicin.
Iran ta illata babban kamfanin Isra'ila
Mun ba ku labarin cewa wani kamfani a Isra'ila ya tabbatar da cewa an kai hari masana’antarsa a kudancin kasar da makami daga Iran.
Gobara ta tashi a yankin masana’antu na Ne’ot Hovav bayan harin, inda jami’an kashe gobara 34 suka yi kokarin shawo kan lamarin.
Hukumomi sun ce an shawo kan gobarar, duk da lalacewar gini, yayin da aka gargadi jama’a su guji yankin saboda sinadarai masu hadari.
Asali: Legit.ng

