A Karshe, Trump zai Hakura da Yakin Iran ko ba Yarjejeniya, Ya Saka Lokaci
- Shugaba Donald Trump ya sake magana kan shirin kawo karshen yakin Iran a cikin kwanaki masu zuwa domin cigaba da harkokinsa
- Abin da ya ba da mamaki a wannan karon shi ne Trump ya ce zai fice daga yakin ko da ba a cimma wata yarjejeniya da Iran ba
- Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum a duniya, Trita Parsi ya bukaci kasashe da al'umma su yi taka tsan-tsan da kalaman Trump
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da shirin da yake yi na kammala yakin da ya kaddamar a Iran a karshen watan Fabarairun 2026.
Ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a fadar White House, inda ya fadi wasu nasrori da ya ce Amurka ta samu a yakin.

Source: Getty Images
Rahoton BBC ya nuna cewa ya shugaba Trump ya yi ikirarin cewa ya samu sauyin gwamnati a Iran bayan kashe wasu shugabanninta.
Trump zai tsayar da yaki da Iran
Shugaban Donald Trump ya ce Amurka na iya kawo ƙarshen hare-haren soji da take kai wa Iran cikin makonni biyu zuwa uku, yana mai cewa ba lallai ba ne Iran ta amince da wata yarjejeniya kafin yaƙin ya ƙare.
“Za mu bar wurin nan ba da daɗewa ba,”
Inji Trump a Fadar White House a ranar Talata, yana mai ƙarawa da cewa hakan na iya faruwa cikin:
“Mako biyu, watakila biyu ko uku.”
Da aka tambaye shi ko ana buƙatar nasarar diflomasiyya da Iran domin kawo ƙarshen rikicin, ya ce ba dole ba ne:
“ Ba dole ba ne Iran ta kulla yarjejeniya, a’a,”
Trump zai yi bayani na musamman
Rahotanni sun nuna cewa Fadar White House ta sanar da cewa shugaba Trump zai yi jawabi ga 'yan Amurka a yau Laraba, 1 ga Afrilun 2026 da yamma.
Bayanan da aka fitar sun nuna cewa manyan abubuwan da zai fada za su kasance masu alaka da yakin da ake a Gabas ta Tsakiya da Iran.

Source: Getty Images
A yi kaffa-kaffa da kalaman Trump
Wani masani kan harkokin waje a cibiyar Quincy Institute, Trita Parsi, ya yi gargadi da cewa ya kamata a yi taka-tsantsan da kalaman Trump.
Ya ce ba zai zama abu mai sauƙi ba Amurka ta janye daga yaƙin da ya bazu a yankin, inda dubban mutane — musamman a Iran da Lebanon — suka mutu, ciki har da fararen hula da dama.
Parsi ya shaidawa Al-Jazeera cewa jadawalin lokacin da ake bayarwa na ci gaba da sauyawa:
“Da farko sun ce yaƙin zai ƙare cikin kwanaki huɗu. Daga baya suka ce makonni uku. Yanzu kuma ana cewa makonni biyu zuwa uku,”
Amurka za ta so diyya a yakin Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa Fadar White House ta fara magana kan neman kudin diyya daga kasashen Larabawa kan yakin Iran.
Rahotanni sun nuna cewa mai magana da yawun White House, Karoline Leavitt ce ta yi maganar yayin amsa tambayoyi kan yakin.
Da aka tambaye ta ko Amurka za ta bukaci diyya, Karoline Leavitt ta ce shugaba Trump zai iya son hakan amma ba za ta ci albasa da bakinsa ba.
Asali: Legit.ng

