Wata Sabuwa: Faransa Ta Yi Mamakin Kalaman da Shugaban Amurka Ya Yi kan Yaki da Iran

Wata Sabuwa: Faransa Ta Yi Mamakin Kalaman da Shugaban Amurka Ya Yi kan Yaki da Iran

  • Faransa ta bayyana cewa har yanzu tana nan kan matsayar da ta dauka tun bayan fara yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da kasar Iran
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin cewa Faransa ta nade hannu, ta ki taimaka masa a yakin
  • Tun farko dai rundunar sojin Faransa ta ba jiragen Amurka izinin amfani da sararin samaniyar kasar, kuma babu wani canza kan hakan har yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

France - Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi martani kan zargin da Shugaba Donald Trump ya yi cewa kasar ta gaza taimakawa Amurka a yakin da take da Iran.

Shugaba Macron ya bayyana cewa ya yi mamakin wannan zargi da Trump ya yi, yana mai cewa Faransa na nan a kan bakarta na goyon bayan Amurka a wannan yaki da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

'Ba da mu ba': Iran ta sake gindaya sharudan tsagaita wuta a yaki da Isra'ila

Shugaba Macron.
Shugaban kasar Amurka, Emmanuel Macron Hoto: Emmanuel Macron
Source: Getty Images

Wane kalamai Trump ya fada kan Faransa?

A rahoton da tashar Al-Jazeera ta tattaro, Faransa ta jaddada cewa matsayarta game da zirga-zirgar jiragen sojan Amurka a sararin samaniyarta bai canza ba.

Tun farko Shugaba Trump ya zargi Faransa da hana jiragen Amurka dauke da kayan sojoji da kayan yaki da ke hanyar zuwa Isra’ila wucewa ta sararin samaniyarta.

Haka zalika ya yi zargin cewa kasar ba ta taimaka ba a yakin Amurka da Isra’ila ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Faransa ta maida martani ga Trump

Fadar shugaban Faransa ta maida martani kan wadannan zarge-zarge na Trump, tana mai cewa ta yi mamakin kalaman da ya fada.

fadar Shugaban Faransa ta ce:

“Mun yi mamaki da wannan rubutu, matsayar Faransa ta kasance daya tun daga farkon wannan yaki zuwa yau, ba a samu wani canji ba a manufofinta."

Wannan batu ya zo ne a lokacin da Spain ta riga ta sanar da haramta wa jiragen sojan Amurka masu alaka da yakin Iran amfani da sararin samaniyarta.

Kara karanta wannan

Trump ya fusata da wasu ƙasashe suka fara juya masa baya a yaki da Iran

Amma kasar Faransa ba ta sanar da irin wannan mataki kai tsaye ba, kamar yadda The Economic Times ta ruwaito.

Shugaba Macron.
Shugaba Emmanuel Macron tare da takwaransa na Amurka, Donald Trump Hoto: Picture alliance
Source: Getty Images

Matsayar Faransa kan yakin Amurka da Iran

Sojojin Faransa sun bayyana tun a farkon watan Maris cewa sun bai wa wasu jiragen Amurka damar amfani da wani sansanin jiragen sama a kudancin kasar, tare da tabbatar da cewa b su da alaka da hare-haren Iran.

Faransa ta nuna cewa ba ta sauya matsayarta ba duk da matsin lamba kuma tana kokarin tsayawa tsaka-tsaki a rikicin.

Amma gwamnatin Faransa ta tabbatar da cewa tana ci gaba da aiki kafada da kafada da Amurka a wasu fannoni da ba su shafi yakin kai tsaye ba.

Amurka ta fara duba yiwuwar janyewa

A baya, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya fara maganar janyewa daga yaki da Iran ta bayan fage bawan shafe wata guda ana gwabzawa.

Trump na shan matsin lamba daga cikin kasarsa kan shiga yaki da Iran, inda miliyoyin mutane suka yi zanga-zanga a Amurka.

Shugaban na Amurka ya ce yana iya kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran ko da kuwa mashigar ruwa ta Hormuz ta ci gaba da kasancewa a rufe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262