Mojtaba Khamenei: Daga Karshe an Bayyana Kasar da Sabon Jagoran Addini na Iran Yake

Mojtaba Khamenei: Daga Karshe an Bayyana Kasar da Sabon Jagoran Addini na Iran Yake

  • Tun farkon fara yakin Amurka, Isra'ila da Iran aka yi ta rade-rade kan lafiyar sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei
  • A wancan lokacin wasu sun rika hasashen an kashe shi yayin da wasu ke cewa ya samu mummunan rauni sakamakon harin da ya kashe mahaifinsa
  • Sai dai, jakadan Rasha a kasar Iran ya kawo karshen jita-jita kan inda Mojtaba Khamenei yake gudanar da rayuwarsa a halin yanzu

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Moscow, Rasha - An samu bayanai kan inda sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei, yake a halin yanzu.

An bayar da tabbacin cewa Mojtaba Khamenei yana cikin ƙasar Rasha amma yana guje wa fitowa fili a bainar jama'a "saboda dalilai da za a iya fahimta."

Mojtaba Khamenei yana kasar Rasha
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Rouhollah Vahdati
Source: Getty Images

Tashar Reuters ta kawo rahoton cewa jakadan Rasha a ƙasar Iran ya bayyana hakan a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Mojtaba Khamenei ya samu mafaka a Rasha

Mojtaba ya maye gurbin mahaifinsa ne, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe lokacin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran fiye da wata guda da ya gabata.

Ita kuwa Amurka ta bayyana cewa ta yi amanna Mojtaba Khamenei ya ji rauni kuma mai yiwuwa ya koma nakasashshe.

Mojtaba Khamenei ya fitar da sanarwa kalilan ne kawai tun bayan zama sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Saƙonsa na farko an bayar da shi ne a cikin wata wasiƙa da aka yi iƙirarin shugaban na Iran ne da kansa ya rubuta ta, yayin da saƙonni na gaba kuma aka isar da su ta wasu hanyoyin da ba a tantance ba.

Rasha tana da kyakkyawar alaƙa da Iran, inda ma suka sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa mai karfi a shekarar da ta gabata.

An yi zargi kan Rasha

Jaridar Jerusalem Post ta ce Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul, ya zargi Rasha da taimaka wa Iran wajen gano wuraren da za a kai wa hari.

Kara karanta wannan

Iran ta shaidawa Amurka tanadin da ta yi wa sojojin da za su kutso cikin kasarta

Ya ce Shugaba Vladimir Putin na fatan yin amfani da yaƙin na Iran a matsayin kawar da hankalin duniya daga harin da yake kai wa Ukraine.

An nuna yatsa ga Rasha kan yakin Iran
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin Hoto: Sergey Fadelchev
Source: Getty Images

Yayin da yake magana da manema labarai a taron ƙasashe bakwai masu karfin tattalin arziki (G7) a ƙasar Faransa, Wadephul ya kuma ce ya tattauna da Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.

Ya bayyana cewa ya tattauna da Marco Rubio ne don bayyana matsayar Jamus, cewa tana shirye ta taimaka wajen taka rawa a mashigar Hormuz bayan an daina faɗa.

Iran ta samu goyon baya a yaki da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Checheniya sun shirya shiga tsundum cikin yakin Amurka da Iran.

Dakarun sojojin sun sanar da shirinsu na zuwa Iran domin tallafa wa dakarun sojojin kasar idan har Amurka ta ƙaddamar da hari ta ƙasa.

Sojojin na Checheniya sun bayyana yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a halin yanzu kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin "yaƙin addini."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng