Iran Ta Samu Tagomashi, Sojojin Wata Kasa Sun Shirya Kawo Mata Dauki kan Yaki da Amurka

Iran Ta Samu Tagomashi, Sojojin Wata Kasa Sun Shirya Kawo Mata Dauki kan Yaki da Amurka

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shirin samun tallafi a yakin da take yi da kasashen Amurka da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Dakarun sojojin Checheniya sun bayyana shirinsu na kawo dauki ga Iran yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin bangarorin da ke yakin
  • Sojojin na Checheniya sun bayyana sharadin da zai sanya su shiga cikin yakin gadan-gadan don taimaka wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Dakarun sojojin Checheniya sun sanar da shirinsu na shiga cikin yakin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Dakarun sojojin sun sanar da shirinsu na zuwa Iran domin tallafa wa dakarun sojojin kasar idan har Amurka ta ƙaddamar da hari ta ƙasa.

Sojojin Checheniya za su taimakawa Iran
Dakarun sojojin Checheniya da ke kasar Rasha Hoto: @presstv
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta shaidawa Amurka tanadin da ta yi wa sojojin da za su kutso cikin kasarta

Meyasa za a kawo dauki ga Iran?

Waɗannan dakarun, waɗanda ke biyayya ga Ramzan Kadyrov, Shugaban jamhuriyar Checheniya ta Rasha, sun bayyana yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a halin yanzu kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin "yaƙin addini."

Sun bayyana yiwuwar shigar su cikin yaƙin kai-tsaye a matsayin Jihadi, wanda yake fafatawa tsakanin nagarta da mugunta domin kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga dakarun Amurka da kawayenta, rahoton India Today ya tabbatar da hakan.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran ba tare da wani dalili ba wanda kuma ya sabawa doka yake ƙara tsananta.

Wasu rahotanni na cewa dakarun Amurka, bisa umarnin Shugaba Donald Trump, suna matsa lamba don ƙaddamar da harin ƙasa bayan gazawar hare-haren sama da aka shafe makonni ana yi.

Ana ci gaba da yaki tsakanin Amurka, Iran

An ƙaddamar da yaƙin ne a ranar 28 ga watan Fabrairu, a tsakiyar tattaunawar nukiliya tsakanin Tehran da Washington, tare da kisan gillar da aka yi wa Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi; Iran ta farmaki sojojin Amurka 500, an ji abin da ya faru

Iran za ta samu dauki a yaki da Amurka
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Hakazalika, an kashe wasu manyan kwamandoji da fararen hula, ciki har da yara ƴan makaranta sama da 170 a garin Minab da ke Kudancin Iran.

A matsayin martani, dakarun sojojin Iran sun gudanar da jerin hare-hare har sau 88 na makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan wuraren sojoji na Isra'ila, da kuma sansanonin Amurka da kaddarorinta a duk faɗin yankin Tekun Fasha.

Iran ta harbo jirgin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sanar da samun nasarar kakkabo wani jirgi mara matuki da ke shawagi a sararin samaniyar kasar.

Rundunar sojojin ta bayyana cewa ta harbo wani jirgin yaki marar matuki (drone) kirar MQ-9 a kusa da birnin Isfahan, tana mai cewa jirgin na “makiyanta Amurka da Isra’ila” ne.

Jirgin MQ-9 Reaper na daga cikin manyan jiragen leken asiri da ake amfani da su wajen kai hare-hare da tattara bayanai, kuma darajarsa na kai kusan Dala miliyan 30 kowanne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng