Ba Wasa: Iran Ta Yi Luguden Wuta kan Amurka da Isra'ila, Ta Farmaki Muhimman Wurare

Ba Wasa: Iran Ta Yi Luguden Wuta kan Amurka da Isra'ila, Ta Farmaki Muhimman Wurare

  • Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta kaddamar da hare-hare kan kadarorin Amurka da Isra'ila
  • IRGC ta kaddamar da rukuni na 88 na hare-haren ramuwar gayya da ta yi wa lakabi da 'Operation True Promise 4'
  • Ta bayyana cewa ta farmaki muhimman wurare ciki har da inda dakarun sojojin Amurka suke boyewa a kasar UAE

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar ruwa ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da wasu ayyukan soja guda huɗu kan wuraren Amurka da Isra'ila.

Rundunar IRGC ta farmaki wuraren ne a sa’o’in farko na ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026, inda ta kai munanan hare-hare a matsayin ɓangare na jerin samame na 88 na Operation True Promise 4.

Iran ta kai hare-hare kan Amurka, Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kawo rahoton kai hare-haren na rundunar IRGC a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki zafi, ta farmaki muhimman wuraren Amurka da Isra'ila

Iran ta farmaki kadarorin Amurka da Isra'ila

Sashen hulɗa da jama’a na IRGC ya sanar da cewa dakarun ruwan sun ƙaddamar da wani "gagarumin" farmaki kan sansanonin makiya.

Tashar Almayadeen English ta ce a cewar sanarwar, an harbi wani jirgin ruwan dakon kaya na gwamnatin Isra'ila, mai suna Express Halfong, da makamai masu linzami masu dogon zango a tsakiyar ruwan tekun fasha (Persian Gulf).

Ta ƙara da cewa, a wani haɗaɗɗen samame na biyu, an yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen lalata wata maboyar dakarun Amurka da ke gaɓar tekun haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE), inda suka fake a wajen sansanonin sojoji saboda tsoron makaman linzamin Iran.

An lalata kayayyakin Amurka

Rundunar ruwa ta IRGC ta kuma lalata wani makami mai yaƙi da jirage marasa matuƙa na runduna ta biyar ta Amurka wanda aka girka a wajen sansaninta kusa da filin jirgin saman Manama da ke Bahrain.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kuma harbi wasu na’urorin ba da kariya na zamani guda biyu a sansanin "Jaber al-Ahmad" na Amurka da ke Kuwait ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Iran ta kaddamar da hare hare masu zafi kan Amurka da Isra'ila

Hakazalika, sanarwar ta IRGC ta jaddada cewa mashigar Hormuz tana ƙarƙashin cikakken ikon dakarunta.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Mafi ƙanƙantar motsi na makiya zai fuskanci martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa."
Iran ta harba makamai kan Amurka da Isra'ila
Makamai masu linzami na Iran Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran na kai hare-hare kan Amurka, Isra'ila

Wannan samame na 88 na Operation True Promise 4 shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren ramuwar gayya na kusan kullum da Iran ke kaiwa tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙin zalunci kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Tun daga wannan lokacin, dakarun sojin Iran ke mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka a faɗin Yammacin Asia da kuma sansanonin Isra'ila.

Sanata ya fadi kuskuren Amurka a yaki da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata a jam'iyyar Democrat, Chris Murphy, ya soki yakin da Amurka ke yi da Iran.

​Sanata Chris Murphy mai wakiltar Connecticut a majalisar dattawa ya bayyana cewa gwamnatin Trump ba ta da “wani takamaiman tsari” na tunkarar Iran.

Chris Murphy ya bayyana cewa Amurka ba ta da wani babban tsari, wanda hakan ya sanya take yin rashin nasara a yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng