Sanatan Amurka Ya Karaya kan Yaki da Iran, Ya Fadi Abin da Ya Sa Kasarsa Rashin Nasara

Sanatan Amurka Ya Karaya kan Yaki da Iran, Ya Fadi Abin da Ya Sa Kasarsa Rashin Nasara

  • Sanata Chris Murphy na jam'iyyar Democrat ya yi tsokaci kan yakin da Amurka ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Chris Murphy ya bayyana cewa Amurka na shan kashi a yakin kuma Iran ce ke yin nasara duk da ikirarin da mahukunta a Washington ke yi
  • Sanatan ya yi gargadin cewa yakin zai iya samar da babban kawance tsakanin Iran da China bayan an kammala shi

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Sanata daga jam’iyyar Democrat, Chris Murphy ya ce Amurka na shan kaye a yaƙin da take yi da Iran ‘cikin jin kunya’

Sanata Chris Murphy ya bayyana cewa gwamnatin Trump ba ta da “wani takamaiman tsari” na tunkarar Iran, kuma tana “shan kaye a wannan yaƙin cikin kunya da rashin dacewa.”

Sanata Amurka ya soki yakin da kasarsa ke yi a Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Sanata Chris Murphy ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Amurka ta sha alwashi, ta fadi abin da ba za ta bari Iran ta mallaka ba

Sanata Chris Murphy babban mamba ne a kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan Amurka.

Yana ɗaya daga cikin karuwar adadin ’yan majalisar da ke kiran da a gaggauta kawo ƙarshen haɗin gwiwar yakin Amurka da Isra'ila a Iran, wanda yanzu ya shiga wata na biyu.

Sanata Murphy ya fadi kuskuren Amurka

Sanata Chris Murphy ya bayyana cewa Amurka ba ta da wani babban tsari, wanda hakan ya sanya take yin rashin nasara a yakin.

"Dabarun yaƙi ba su da amfani idan babu babban tsari. Shi ya sa ‘dabarar’ kashe dubban mutanen Vietnam ta Arewa ko Taliban ba ta tsinana komai ba face taimaka wa makiyinmu. Dabarun ba su da wani babban tsari."
“Haka abin yake a Iran. Dabarunmu sun gaza, kuma shi ya sa Iran ke samun nasara.”

- Sanata Chris Murphy

Meyasa Iran ke yin nasara?

Ya kuma nuna cewa duk da cewa Amurka ta lalata da dama daga cikin ƙarfin sojojin sama da na ruwa na Iran, ta gaza lalata dukkan jirage marasa matuƙa da kwale-kwalen kai harin kunar bakin wake na Iran, don haka hare-haren har yanzu suna nan suna ci gaba.

Kara karanta wannan

Bayan kwadayin man fetur, an gano abin da zai kai sojojin Amurka cikin Iran

"Iran tana ɓoyewa tare da sauya wa makamai masu linzaminta da wuraren harba su guri. Da alama babu wata hanya ta kawo ƙarshen iyawarsu na farmakar sansanoninmu (wani ɓangare saboda Rasha na taimaka musu wajen nuna musu inda za su harba)"
"Da kuma wuraren samar da makamashi a yankin (makaman linzaminsu na haddasa matsalar makamashi ta duniya)."

- Sanata Chris Murphy

Sanata Chris Murphy ya soki yakin Amurka kan Iran
Sanata Chris Murphy na jam'iyyar Democrat a Amurka Hoto: @ChrisMurphyCT
Source: Twitter

Sanatan Amurka ya yi gargadi

Sanata Chris Murphy ya yi gargaɗin cewa yaƙin zai haifar da “ƙwaƙƙwaran ƙawance tsakanin China da Iran”.

Yaƙin zai haifar da ƙwaƙƙwaran ƙawance tsakanin China da Iran. Bayan Trump ya gaji da yaƙin, Iran da China za su kulla yarjejeniya."

"Wani ɓangare na yarjejeniyar zai iya zama rage wa China “harajin wucewa” ta Mashigin ruwa (Strait), a madadin taimakon da za a ba Iran wajen sake gina rundunarta ta ruwa, ta sama, da makamai masu linzami."

- Sanata Chris Murphy

Amurka ta sha alwashi kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi maganganu kan yakin da kasarsa ke yi da Iran.

Marco Rubio ya bayyana cewa Amurka ba za ta bari gwamnatin Iran ta taɓa samun damar mallakar makaman nukiliya ba.

Ministan ya ce gwamnatin Iran na son mallakar makaman nukiliya ne domin yi wa duniya barazana da tsoratarwa, amma ba za su taɓa barin hakan ta faru ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng