Tirkashi: Amurka Ta Sha Alwashi, Fadi Abin da ba Za Ta Bari Iran Ta Mallaka ba

Tirkashi: Amurka Ta Sha Alwashi, Fadi Abin da ba Za Ta Bari Iran Ta Mallaka ba

  • Ana ci gaba da gwabza fada a tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya fito ya yi magana kan yakin wanda aka shafe fiye da wata daya ana fafatawa
  • Marco Rubio ya bayyana cewa akwai abin da Amurka ba za ta bari Iran ta mallaka ba yayin da ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi magana kan yakin da kasarsa ke yi da Iran.

Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Iran ba za ta taɓa samun damar mallakar makaman nukiliya ba.

Amurka ta sha alwashi kan Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka da sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B
Source: Getty Images

Marco Rubio ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da tashar Aljazeera wadda aka fitar a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Me Amurka ta ce kan Iran?

Mininistan ya ce gwamnatin Iran na son mallakar makaman nukiliya ne domin yi wa duniya barazana da tsoratarwa, amma ba za su taɓa barin hakan ta faru ba.

Ya bayyana cewa dole ne Iran ta ɗauki kwararan matakai wajen watsi da shirinta na nukiliya da kowane irin buri na mallakar makaman nukiliya.

Hakazalika, Marco Rubio ya ce dole ne Iran ta daina kera dukkan jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami.

Marco Rubio ya soki Iran

Ministan harkokin wajen na Amurka ya kuma soki shirin makamai masu linzami na Iran, inda ya yi nuni musamman ga makaman linzaminta masu gajeren zango.

Marco Rubio ya kuma yi magana kan yadda Iran ke amfani da waɗannan makamai kan maƙwabtanta na yankin Gulf a cikin watan da ya gabata.

“Makamai masu linzami masu gajeren zango da Iran ke harbawa suna da manufa guda ɗaya kawai: kai hari ga Saudiyya, UAE, Qatar, Kuwait, da Bahrain."

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Amurka ta fadi lokacin ficewa daga Iran, ta jero nasarorin da ta samu

- Marco Rubio

Ya ƙara da cewa, dole ne Iran ta “daina kera jirage marasa matuƙa da makaman linzami da muka gani kwanan nan.”

Iran ta yi watsi da damar tattaunawa

Marco Rubio ya ce Iran ta samu damar yin amfani da diflomasiyya domin hana harin da Amurka da Isra'ila suka kai mata, amma ta gaza yayin tattaunawa.

Marco Rubio ya soki gwamnatin Iran
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio Hoto: picture alliance
Source: Getty Images

Ya ce a halin yanzu ana nan ana tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin.

“Da mun iya yin hakan tun da farko. Ina nufin, yi tunanin gwamnatin Iran wadda, maimakon kashe biliyoyin daloli wajen tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci da tara duk waɗannan makaman, ta saka waɗannan kuɗaɗen a cikin Iran, domin mutanen Iran, yadda ba za su fuskanci ƙarancin ruwa ba, yadda tattalin arzikinsu zai samar da guraben ayyuka."
"Mutanen Iran mutane ne masu ban mamaki — suna da basira da hazaka sosai. Amma gwamnatinsu ce take zama matsala, kuma maimakon haka, sun zaɓi kashe arzikin ƙasarsu wajen tallafa wa Hezbollah da Hamas da mayakan sa-kai na Shi’a a cikin Iraki.”

Kara karanta wannan

Ana cikin gwabza yaki, Trump ya fasa kwai kan babbar kyautar Iran ga Amurka

- Marco Rubio

Shirin sojojin Iran kan Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Iran sun shirya gudanar da aikin bazata kan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Manyan sojojin na Iran da suka ƙunshi dakarun runduna ta 65 ta Airborne ta rundunar sojoji, wadda aka sani da NOHED, suna shirye-shirye don kai wa Amurkawa babban hari.

Dakarun na NOHED za su kai hare-haren a wani aikin haɗin gwiwa da dakarun musamman na Saberin na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng