Trump Ya Fito da Maitarsa a Fili, Ya Fadi Me Ya ke Nema a Iran

Trump Ya Fito da Maitarsa a Fili, Ya Fadi Me Ya ke Nema a Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana babban abin da ya ke son samu a Iran bayan kaddamar da yaki da ya yi a watan Fabrairun 2026
  • Trump ya bayyana haka ne yayin wani taro a kasar Amurka yayin da yake korafi game da toshe mashigar Hormuz da Iran ta yi bayan fara yakin
  • Hakan na zuwa ne yayin da yakin Iran da Amurka/Isra'ila ke cigaba bayan shafe kwanaki sama da 30 ana gwabza fadan da ya shafi kasashe da dama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Donald Trump ya ce abin da ya fi so shi ne karɓar man fetur din Iran, yayin da ƙasar ke ci gaba da musayar hare-hare da Isra'ila da Amurka.

Iran na daga cikin ƙasashen OPEC, kuma tana da ɗaya daga cikin manyan masu arzikin man fetur a duniya, inda ta fitar da kusan ganga miliyan 208 na mai a shekarar 2024, bayan Venezuela da Saudiyya.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: An kawo dabarar hambarar da Trump daga shugaban kasar Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na wani jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya bayyana babban abin da yake so a Iran ne a wata hira a wata hira da aka yi da shi a wata tattaunawa da Financial Times.

Abin da Donald Trump ke so a Iran

A wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi, Trump ya ce zai fi so ya karɓi man fetur na Iran, duk da cewa wannan buri bai cikin manufofin yaƙin da ya bayyana a bainar jama’a.

“Gaskiya idan zan faɗa maka, abin da na fi so shi ne mu karɓi man fetur na Iran, amma wasu wawaye a Amurka suna cewa me ya sa ake yin hakan,”

Inji Trump

Maganar kwacewa Iran Kharg

CNN ta rahoto cewa shugaba Donald Trump ya kuma ambaci yiwuwar ƙwace tsibirin Kharg, wanda shi ne cibiyar fitar da man fetur ta kasar Iran.

“Wataƙila mu karɓi tsibirin Kharg, wataƙila kuma ba za mu yi ba. Muna da zabuka da dama,”

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Amurka ta fadi lokacin ficewa daga Iran, ta jero nasarorin da ta samu

Inji shi, yana mai ƙarawa da cewa hakan na iya buƙatar kasancewar sojojin Amurka a wurin na wani lokaci.

An kiyasta cewa tsibirin na da ƙarfin ajiyar mai da ya kusan ganga miliyan 30, kuma yana sarrafa kusan kashi 90 cikin 100 na man da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Tsibirin Kharg da ke Iran.
Tsibirin Kharg da Trump ke son kwacewa a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun a watan Janairun 2026, Amurka ta kama shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, tare da sanar da cewa ta karɓi iko da harkokin man fetur na ƙasar.

Iran: Uganda za ta taimaki Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa kasar Uganga ta sanar da cewa tana shirye ta taimakawa Isra'ila a yakin da ta ke gwabzawa da Iran.

Duk da cewa Amurka ta hada kai da Isra'ila wajen yakar Iran, babban hafsun sojan Uganda ta ce ba za su zuba ido a gama da Tel Avid ba.

Sojan kasar Uganda ya bayyana cewa Isra'ila ta taimaka masu a baya, saboda haka lokaci ya yi da za su rama alherin da aka masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng