Ana Tsaka da Zargin Isra’ila da Cin Zarafin Kiristoci, an Ci Mutuncin Babban Fasto
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan sanda a kasar Isra'ila sun hana babban Fasto shiga cocin 'Holy Sepulchre'
- An hana limami shiga cocin ne domin gudanar da ibadar 'Palm Sunday' da aka gudanar a yau Lahadi 29 ga watan Maris, 2026
- Haramcin taruka sakamakon yaki ya jawo dakatar da bukukuwan addini a Jerusalem da kewaye wanda ya shafi Musulmi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Jami’an ‘yan sandan Isra’ila sun hana wani babban Fasto shiga coci a kasar domin taron ibadar Kiristoci.
An hana Pierbattista Pizzaballa, babban limamin Katolika a Jerusalem, shiga cocin 'Holy Sepulchre' domin gudanar da ibadar 'Palm Sunday'.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata sanarwa daga cocin wanda France 24 ta samu inda ta ce wannan ne karo na farko cikin daruruwan shekaru da aka hana shugabannin addini gudanar da wannan ibada a wurin mai tsarki.
An hana Fasto shiga coci a Isra'ila
An tabbatar da cewa lamarin ya faru da safiyar yau Lahadi 29 ga watan Maris din shekarar 2026 yayin da Faston ke kan hanyarsa ta zuwa ibada.
Sanarwar ta ce:
“Da safiyar yau, ‘yan sandan Isra’ila sun hana shugaban cocin Katolika na yankin Kudus, Mai Martaba Kardinal Pierbattista Pizzaballa, shiga Cocin Holy Sepulchre da ke Kudus, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gudanar da ibadar Palm Sunday.”
“Sakamakon haka, kuma a karon farko cikin ƙarnuka da dama, an hana shugabannin cocin gudanar da ibadar Palm Sunday a Cocin Holy Sepulchre.
“Wannan lamari wani babban abin damuwa ne kuma yana nuna rashin la’akari da jin daɗin biliyoyin mutane a duniya, waɗanda a wannan mako suke kallon Kudus a matsayin cibiyar ibadarsu.”

Source: Facebook
yadda aka soki matakin a duniya
An bayyana matakin a matsayin abin takaici da ke nuna rashin girmama mabiya addini miliyoyi a duniya da ke kallon Jerusalem a wannan lokaci.
Firaministar Italiya, Giorgia Meloni, ta soki matakin inda ta kira shi cin mutunci ga mabiya addinin Kirista.
Ministan harkokin wajen Italiya ma ya gayyaci jakadan Isra’ila domin neman bayani kan lamarin, cewar rahoton Al Jazeera.
Tun bayan barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya, hukumomin Isra’ila sun hana manyan taruka a wuraren ibada ciki har da coci, masallatai da sinagog.
An takaita taruka zuwa kusan mutane 50 kawai, lamarin da ya sa aka soke jerin gwanon Palm Sunday da aka saba yi daga Mount of Olives zuwa cikin Jerusalem.
Cocin ta ce duk da cewa shugabannin addini sun bi dukkan dokokin da aka kafa, hana Cardinal din shiga ya saba ka’idojin ‘yancin ibada da adalci.
An caccaki Netanyahu kan taba Kiristoci
A baya, an ji cewa Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya jawo ce-ce-ku-ce bayan kalamansa kan Annabi Isa (AS) da Genghis Khan.
Jama’a sun caccaki kalamansa a shafukan sada zumunta, suna zargin sa da nuna ƙiyayya ga Kiristoci a kasar wanda ke da mafi yawan mabiya addinin Yahudanci.
Netanyahu ya musanta zargin, yana cewa bai taba raina Annabi Isa ba kuma Kiristoci na samun kariya a Isra’ila kuma babu inda ya taba mutuncinsu.
Asali: Legit.ng

