Yaki da Iran: An Kawo Dabarar Hambarar da Trump daga Shugaban Kasar Amurka
- Scott McConnell, mawallafin babbar jarida a Amurka ya bukaci JD Vance da ya amince da tsarin hambarar da Shugaba Donald Trump
- Editan ya ba da shawarar cewa Vance, wanda shi ne mataimakin shugaban kasa a yanzu, ya karbi mulki daga Trump saboda gazawarsa
- Duk da wannan kira, sababbin bayanai sun nuna cewa 90% na magoya bayan MAGA suna nan tare da Trump a yakin da yake yi da Iran
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Babban editan mujallar The American Conservative, Scott McConnell, ya fito da wani tsari dake kira ga mataimakin shugaban kasa, JD Vance, ya karɓi ragamar mulki daga hannun Donald Trump.
McConnell ya wallafa a shafinsa na X cewa ya kamata Vance ya yi amfani da sashe na 25 na kundin tsarin mulkin Amurka, wanda ke ba da damar tsige shugaban ƙasa idan aka iske ba shi da lafiyar jagoranci.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Amurka ta fadi lokacin ficewa daga Iran, ta jero nasarorin da ta samu

Source: Getty Images
An kawo tsarin hambarar da Trump daga mulki
Wannan shawara tana zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da takun-saƙa kan yaƙin da Amurka ke fafatawa da ƙasar Iran, wanda ya raba kan masana da 'yan siyasa a ƙasar.
A cikin tsarin nasa, McConnell ya bayyana cewa ya kamata Vance ya zaɓi Sanata Chris Murphy, wanda ɗan jam'iyyar Democrat ne, a matsayin mataimakinsa domin gudanar da mulkin haɗin gwiwa.
Ya bayyana cewa zaɓar Murphy zai kasance mataki mai kyau saboda sanatan baya goyon bayan yaƙi, sannan yana da basirar da za ta taimaka wajen kwantar da tarzomar da ake ciki.
McConnell ya ƙara da cewa ya kamata Vance ya yi amfani da damarsa ta kafafen yaɗa labarai wajen bayyana wa duniya dalilin da ya sa wannan mataki na karɓar mulki ya zama dole.
Kalli sanarwar McConnell a nan kasa:
Martani daban-daban kan tsarin tsige Trump
Wannan kiran na McConnell ya janyo martani masu zafi daga masu amfani da shafukan sada zumunta, inda wasu suka bayyana shawarar tasa a matsayin "mahaukaciyar dabara" dake son ruguza gwamnati.
Wasu masu sharhi sun nuna takaicinsu kan yadda wasu masu ra'ayin mazan jiya suke son miƙa mulki ga jam'iyyar Democrat a daidai lokacin da jam'iyyarsu ta Republican ke samun nasara, in ji rahoton Yahoo News.
Sai dai McConnell ya nace kan cewa wannan ita ce kawai hanyar da za a iya dakatar da abin da ya kira salon mulkin Trump dake jefa ƙasar cikin haɗari musamman ta fuskar yaƙi.

Source: Getty Images
Matsayar MAGA kan yaƙin Amurka da Iran
Duk da wannan kira na neman tsige Trump, binciken jin ra'ayin jama'a na kwanan nan ya nuna cewa magoya bayan tafiyar "Make America Great Again" (MAGA) suna nan tare da Trump.
Wani bincike da kafar NBC News ta gudanar ya nuna cewa 90% na magoya bayan MAGA suna goyon bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai wa ƙasar Iran a halin yanzu.
Haka kuma, binciken CNN ya tabbatar da cewa magoya bayan Trump sun fi amincewa da matakan da yake ɗauka kan Iran fiye da sauran Amurkawa waɗanda ba sa goyon bayan tafiyar tasa.
Zanga zangar adawa da Trump ta barke
A wani labari, mun ruwaito cewa, miliyoyin mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Donald Trump a birane daban-daban na kasar Amurka.
Masu zanga-zangar sun bukaci a dakatar da matakan takura wa bakin haure da kuma kawo karshen yakin da ake yi da kasar Iran.
Fadar White House ta yi Allah wadai da wannan zanga zanga, inda ta bayyana ta a matsayin taron mutane masu kyamar gwamnati.
Asali: Legit.ng

