Miliyoyin Mutane Sun Fita Zanga Zanga a Amurka, Trump na Fuskantar Babbar Matsala

Miliyoyin Mutane Sun Fita Zanga Zanga a Amurka, Trump na Fuskantar Babbar Matsala

  • Miliyoyin mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Donald Trump a birane daban-daban na kasar Amurka
  • Masu zanga-zangar sun bukaci a dakatar da matakan takura wa bakin haure da kuma kawo karshen yakin da ake yi da kasar Iran
  • Fadar White House ta yi Allah wadai da wannan zanga zanga, inda ta bayyana ta a matsayin taron mutane masu kyamar gwamnati

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Miliyoyin mutane ne suka taru a faɗin ƙasar Amurka a ranar Asabar domin gudanar da zanga-zangar "No Kings" karo na uku domin adawa da Shugaba Donald Trump.

A birnin Washington, masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa filin National Mall dake gaban ginin tunawa da Lincoln kafin su yi turjiya a kusa da ginin Washington Monument.

Kara karanta wannan

Trump na cikin yaki da Iran, gagarumar matsala ta tunkaro shi a Amurka

Zanga zangar adawa da gwamnatin Trump ta barke a Amurka
Miliyoyin mutane sun fita zanga zangar adawa da Trump a Amurka. Hoto: Scott Olson/Getty Images
Source: Getty Images

Zanga zangar adawa da Trump a Amurka

Tom Schneider, wanda ya yi tattaki daga Connecticut, ya bayyana cewa yana ganin ya zama dole ya fito ya bayyana adawarsa domin kare tsarin dimuƙuradiyya, in ji rahoton CNN.

Masu zanga-zangar "No Kings" sun bayyana wa manema labarai cewa sun fito domin neman a daina musgunawa baƙin haure da kuma dakatar da yaƙin Iran.

Wani mai zanga-zanga a Minneapolis ya bayyana cewa babban dalilin fitowarsa shi ne yadda tsarin dimuƙuradiyya yake fuskantar barazana a ƙarƙashin gwamnatin Donald Trump.

Haka kuma, masu zanga-zangar sun koka kan yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa a faɗin duniya, suna masu cewa hakan ya jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali.

Zanga-zanga: Martanin Fadar White House

Fadar White House ta yi Allah-wadai da waɗannan zanga-zangoyi, inda kakakin fadar, Abigail Jac, ta bayyana su a matsayin taron mutane masu fama da ciwon ƙyamar Trump, in ji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Trump zai tafi Venezuela neman takarar shugaban kasa

A birnin Chicago, wani tsohon soja mai suna Chris Holy da ɗansa Nicholas sun bayyana cewa rashin adalcin da suke gani a ƙasar ne ya tilasta musu fitowa zanga-zanga.

Har ila yau, Yohanna, wata mai zanga-zanga a Manhattan, ta bayyana cewa idan Amurkawa suna son dimuƙuradiyya, to dole ne su shiga ciki domin ceto ta daga rugujewa yau.

Haɗin kan kungiyoyin ma'aikata a Portland

Fedrick Ingram, babban jami'i a ƙungiyar malaman Amurka, ya tabbatar da cewa ƙungiyarsu ta fito a birnin Portland domin yaɗa saƙon fatan alheri maimakon tsoro ga jama'a.

Masu zanga-zanga a Amurka sun nuna adawa da manufofin shugaban kasa Donald Trump.
Miliyoyin mutane sun fita zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Trump a Amurka. Hoto: Scott Olson/Getty Images
Source: Getty Images

Ingram ya bayyana cewa ko a baya ƙasar ta taɓa samun miyagun dokoki da 'yan siyasa, amma haɗin kan jama'a ne ya kasance makamin da yake fitar da su.

An shirya zanga-zangoyi sama da 3,000 a dukkan jihohi 50 na Amurka a wannan rana, wanda hakan ke nuna girman rashin jin daɗin jama'a da salon mulkin.

Kalli bidiyon zanga-zangar da Sky News ta wallafa a nan kasa:

Matsalar da Trump yake fuskanta a Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ya nuna matsayar wasu Amurkawa game da yakin da Donald Trump yake yi da Iran.

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

Binciken jin ra'ayin ya nuna cewa kashi ɗaya ne kawai cikin huɗu na Amurka suka amince da hare-haren da Trump ya kai Iran, da ya yi sanadin mutuwar Ayotallah Khamenei.

Binciken ya bayyana cewa kusan rabin Amurkawa, har da kashi ɗaya cikin huɗu na ƴan jam'iyyar Republican, na ganin Shugaba Trump ya cika gaggawar yin amfani da ƙarfin soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com